Rikici: ‘Yan sanda sun fesa barkonon tsohuwa a wurin zaben fidda-gwanin sanatocin APC a Jigawa

Rikici: ‘Yan sanda sun fesa barkonon tsohuwa a wurin zaben fidda-gwanin sanatocin APC a Jigawa

Rikici ya kaure a yayin da ake gudanar da zaben fidda-gwanin jam’iyyar APC na sanata a Karamar Hukumar Hadejia dake Jihar Jigawa.

Lamarin ya nemi wuce kima har sai da ta kai ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa akan masu zabe da shugabannin jam’iyya domin a samu kura ta lafa.

Hakan ya afku ne a wajen zaben dan takarar sanata a shiyyar Jigawa ta Arewa, wanda aka gudanar a filin wasan kwallon kafa na garin Hadeja.

Rikici: ‘Yan sanda sun fesa barkonon tsohuwa a wurin zaben fidda-gwanin sanatocin APC a Jigawa
Rikici: ‘Yan sanda sun fesa barkonon tsohuwa a wurin zaben fidda-gwanin sanatocin APC a Jigawa
Asali: UGC

Barkewar rikicin ya faru ne bayan da wasu masu zabe suka fara korafin cewa an baddala sunayen wadanda za su jefa kuri’a.

Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Ibrahim Hassan na daga cikin wadanda ke neman takarar sanata. Akwai kuma Ahmed Garba, Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Jigawa da kuma Mohammed Husseini.

KU KRANTA KUMA: Dalilin ganawarmu da Buhari - Rochas

Daga Husseini ya bayyana janyewar sa daga takarar a dalilin zargin da ya yi cewa an cusa sunayen masu zabe wadanda ba bisa doka ba.

A baya Legit.ng ra rahoto cewa shugaban kwamitin majalisar dattawa akan man fetur, Sanata Kabiru Garba Marafa ya goyi bayan hukuncin soke zaben fidda gwani na gwamna da kwamitin jam’iyyar APC tayi jiya a jihar Zamfara, duk da cewar shi ne ke kan gaba a dukkanin mazabun da aka gudanar da zaben.

Marafa wanda ya kasance daya daga cikin yan takaran a wata sanarwa ya ga laifin Gwamna Yari kan rikicin da ya balle a wasu yankunan jihar lokacin zaben.

Yace kira ga ci gaba da zaben da Yari da abokan tafiyarsa suka yi duk da rikicin da ya balle rashin tunani ne da rashin hankali da kuma mugunta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel