Shirin wasan kwaikwayo za a yi da su - Dan Najeriya da aka kama da dubban dalolin bogi (hoto)

Shirin wasan kwaikwayo za a yi da su - Dan Najeriya da aka kama da dubban dalolin bogi (hoto)

Wani dan Najeriya na bawa jami'an tsaron kasar Afrika ta kudu hadin kai bayan an kama shi da jabun dalolin kasar Amurka da yawansu ya kai $251,000.

Henry Omoaka, mai shekaru 51 an kama kama shi ne a da yammacin ranar Laraba a gidansa dake rukunin gidajen Malaika a South B. An samu kullin hodar ibilis yayin da ake binciken gidansa.

Bayan an kama shi, Omoaka ya shaidawa jami'an tsaro cewar shi mai sana'ar rubuta fina-finai ne kuma za a yi amfani da kudin ne domin shirin wani wasan kwaikwayo.

Shirin wasan kwaikwayo za a yi da su - Dan Najeriya da aka kama da dubban dalolin bogi (hoto)
Dan Najeriya da aka kama da dubban dalolin bogi
Asali: Twitter

Sai dai da aka tambaye shi sunan wasan kwaikwayon, ya ce ba zai iya tunawa ba.

Daga bisani bayan ya fuskanci matsin lamba sai ya amsa cewar kudin ba iya nasa bane shi kadai, akwai kason wasu 'yan Najeriya da kuma 'yan kasar Afrika ta kudu.

DUBA WANNAN: Ya mare shi, shi kuma ya cije shi: Hadiman Buhari biyu sun yi fada a kan zaben fitar da dan takarar gwamna a APC

Bincike ya nuna cewar tuni wa'adin takardun Omoaka na izinin zama a kasar suka kare.

Jami'an tsaro sun bayyana cewar masu yin jabun kudi na amfani da su ne wajen damfarar 'yan kasuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel