An kashe makiyayi a Adamawa, an kuma sace masa shanu 16

An kashe makiyayi a Adamawa, an kuma sace masa shanu 16

- An saba sace shanu a dazukan kasar nan

- Makiyaya kan kai farmaki garuruwa kan mutane da basu ji ba basu gani ba

- Gwamnati na iyakar kokarin kawo kasrshen matsalar

An kashe makiyayi a Adamawa, an kuma sace masa shanu 16
An kashe makiyayi a Adamawa, an kuma sace masa shanu 16
Asali: Facebook

Hukumar 'yansandan jihar Adama, ta bakin kakakinta, ta tabbatar da kisan wani makiyayai a yankin Kademun village dake Demsa Local Government Area a jihar ta Adamawa.

Bayan haka kuma ta tabbatar da an saci shanu har 16 lamari da kakakin hukumar, Usman Abubakar, ya tabbatar da faruwarsa a 26 ga watan satumba.

DUBA WANNAN: Yadda Kwankkwaso zai koyi siyasa daga Tinubu

Da suka kai samame yankin kuma, a cewarsa, mahara sun kai musu hari inda suka yi sa'ar kama babura hudu daga hannun wadanda ake zargi, an kuma kai wa hakimin garin Alhamdu Teneke rahoto don ya sanya baki a lamarin.

Su dai makiyaya sun ce shanunsu da aka sace a yankin sun kai 20, kumma suna jira a bi masu hakkinsu.

Matsalar makiyaya da manoma ta kashe mutane da yawa musamman a shekarun nan na kabilanci da bangaranci a tsakiyar kasar nan.

Na nan tafe: Shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Wannan cigaba na kuma da fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewanku tare da mu

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel