‘Yaradua da Sanatan Katsina sun rasa tikitin ‘Dan Majalisan APC

‘Yaradua da Sanatan Katsina sun rasa tikitin ‘Dan Majalisan APC

NAIJ Hausa ta samu labari cewa Sanata Umaru Ibrahim Kurfi wanda ke wakiltar Katsina ta tsakiya a Majalisar Dattawa ya fadi zaben fitar da gwani na APC inda ya zo na uku a zaben da aka shirya jiya.

‘Yaradua da Sanatan Katsina sun rasa tikitin ‘Dan Majalisan APC
Sanata Kurfi ya sha kasa a hannun tsohon Shugaban FERMA Barkiya
Asali: UGC

Injiniya Kabiru Abdullahi Barkiya ya samu tikitin Sanata a karkashin Jam’iyyar APC inda ya tashi da kuri’u 1466. Wanda ya zo na biyu a zaben dai shi ne Abdulaziz Yaradua wanda ya tashi da kuri’a sama da 900 inji Malamin aikin zaben.

Sanata Umaru Kurfi wanda yake kan kujerar a yanzu haka ya zo na uku ne bayan ya samu kuri’a 141 rak. Kabiru Abdullahi Barkiya wanda zai rikewa APC tuta a zaben 2019 dai tsohon Shugaban Hukumar FERMA ne masu gyaran hanyoyi.

KU KARANTA: Yakubu Dogara ya samu tikitin takara a PDP bayan ya bar APC

Wannan sakamako dai ya ba jama’a mamaki sai dai kuma da alamu Sanatan da ke kan kujerar Sanata na Yankin Katsina ta Kudu watau Abu Ibrahim ya janye takarar sa. Hakan zai ba Jam’iyyar APC daman mikawa wani 'Dan takarar tikiti.

A Yankin Katsina ta Arewa kuwa inda nan ne Mazabar Shugaban kasa Buhari, ana tunani cewa Sanatan da ya lashe zabe kwanaki ne watau Ahmad Babba Kaita zai cigaba da rike kujerar. Daga cikin masu neman takarar akwai Umar Katsayal.

Kwanaki kun ji cewa ana rikici a Kaduna bayan an hana wasu takarar Sanata a Jihar inda Jam’iyyar APC mai mulki ta ba Sanatan da ke-kan kujera a yanzu watau Shehu Sani tikitin takara a sama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel