2019: An shiga ganawar sirri tsakanin Obasanjo da Tambuwal

2019: An shiga ganawar sirri tsakanin Obasanjo da Tambuwal

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya shiga wata ganawar sirri da tsohon gaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, a gidansa da ke garin Abeokuta.

A cigaba da rangadin da yake yi domin saduwa da daliget da zasu yi zaben fidda ‘yan takara, Tambuwal ya gana da tsofin shugaban kasa da suka hada da Ibrahim Babangida (IBB).

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar tsohon shugaban kasar Najeriya da ya sha kaye a zaben shekarar 2015, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewar yanzu haka Najeriya ce shelkwatar talauci ta duniya, domin babu kasar da take da yawan matalauta da Najeriya keda su yanzu haka.

2019: An shiga ganawar sirri tsakanin Obasanjo da Tambuwal
Tambuwal
Asali: Facebook

Jonatahan na wadannan kalamai ne cikin sakonsa day a fitar a shafinsa na tuwita na taya Najeriya da ‘yan kasar murnar zagayowar ranar samun ‘yan ci a karo na 58.

DUBA WANNAN: Zaben fidda 'yan takara: Yadda aka mamura Kawu Sumaila har Kabiru Gaya ya kayar da shi

A sakon nasa, bayan ya yi murnar zagayowar wannan rana, ya kuma bayyana juyayinsa bisa yadda yanzu Najeriya ta zama shelkwatar fatara da talauci a fadin duniya baki daya.

Sai dai tsohon shugaba Jonathan ya karfafawa ‘yan Najeriya gwuiwar da kalaman cewar halin fatara da talauci da kasar ke fuskanta ba zai dore ba saboda irin yadda mutanen Najeriya ke da jajircewa wajen neman na kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng