Zaben cikin gida: Yadda aka shiryawa Kawu Sumaila gadar zare har Kabiru Gaya ya kayar da shi

Zaben cikin gida: Yadda aka shiryawa Kawu Sumaila gadar zare har Kabiru Gaya ya kayar da shi

Rahotanni daga jihar Kano da jaridar Legit.ng ta samu sun tabbatar da cewar an shirya dabarar bayar da sanarwar dage zaben dan takarar sanatan Kano ta kudu a kafafen yada labarai ne domin magoya bayan Kawu Sumaila su bar wurin zabe.

Wani masoyin Kawu, Ahmed Deedat, ya bayyana cewar suna filin gudanar da zaben fitar dad an takara ne sai suka ji an bayar da sanarwar dage zaben a gidan Radiyo amma bayan magoya bayan Kawu sun koma gida sai suka ji ana sanar da sakamakon cewar Kabiru Gaya ya lashe zaben takarar kujeran sanatan Kano ta kudu a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Wannan lamari ya matukar dugunzuma masoya Kawu a yankin Kano ta kudu hart a kai ga suna ikirarin kin kada kuri’a ga APC a zaben sanata da za a yi a shekarar 2019.

Zaben cikin gida: Yadda aka shiryawa Kawu Sumaila gadar zare har Kabiru Gaya ya kayar da shi
Kawu Sumaila da Kabiru Gaya
Asali: Twitter

A wani labarin mai alaka da irin abinda ya faru a APC ga Kawu Sumaila, shugaban jam'iyyar PDP a Kano, Masa'ud El-jubrin Doguwa, ya yi watsi da sakamakon zaben fitar da dan takarar gwamna da tsagen Kwankwasiyya ya yi a gidan tsohon gwamna, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Da yake magana jiya, Talata, a madadin ragowar 'yan takarar kujeru daban-daban a jihar Kano, Doguwa ya bayyana zaben da aka yi a gidan Kwankwaso da cewar haramtacce ne da bashi da matsuguni a tsarin siyasa balle dokar jam'iyya.

DUBA WANNAN: 2019: Gwamna dake takarar gwamna a PDP ya koma APC

Kazalika ya zargi uwar jam'iyyar PDP ta kasa da bin tsarin mutum daya kacal duk da kasancewar sune suka rike jam'iyyar a matakin jiha lokacin da kusan dukkan jiga-jigan 'ya'yanta suka fice.

Doguwa ya kalubanci uwar jam'iyyar PDP da ta zama mai adalci ga dukkan 'yan jam'iyyar da suka sayi fam din takara ta hanyar gudanar da zabe na adalci da kowa zai gamsu da sakamakon sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel