An garkame wata Uwargida da laifin bincike cikin Wayar Salula ta Mai gidan ta

An garkame wata Uwargida da laifin bincike cikin Wayar Salula ta Mai gidan ta

Wani rahoto mai cike da ban mamaki da muka samu ya bayyana cewa, wata babbar kotu can daular Larabawa ta Tsakiya ta yankewa wata uwargida hukuncin dauri na zama a gidan kaso har na tsawon watanni uku bisa laifin yiwa Mijinta hawan kawara.

Laifin wannan Mata kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito bai wuci leke gami da bincike cikin Wayar Salula ta Mai gidanta ba tare da masaniyarsa ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, Mai gidan wannan Mata shi ya shigar da korafin har gaban Kuliya domin neman hakki da koken sa na cewa ta ketare masa gona gami da leken asiri.

Sai dai a yayin zartar da hukuncin ta, Kotun dake zamanta a yankin Ras Al Khaimah ta kama wannan Mata dumu-dumu da aikata laifin da ake tuhumarta.

An garkame wata Uwargida da laifin bincike cikin Wayar Salula ta Mai gidan ta
An garkame wata Uwargida da laifin bincike cikin Wayar Salula ta Mai gidan ta
Asali: UGC

Cikin zayyana korafinsa ga babbar Kotun, mijin wannan Mata ya bayyana cewa, Uwargidansa ta wanki duk wani sirri na ajiya da ya yi cikin wayarsa ta Salula ta hanyar amfani da fasahar zamani domin bincike da leka masa asiri.

KARANTA KUMA: Ajimobi ya lashe zaben fidda gwanin takarar Kujerar Sanatan Oyo ta Kudu

Kamar yadda Mijin wannan Mata ya bayyana, Uwargidan sa ta aikata wannan mummunar dabi'a ne a yayin da yake sauke gajiyarsa a lokacin bacci.

Legit.ng da sanadin shafin jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumomin Daular Larabawa su kan daga gira tare da murza gashin baki dangane da wannan mummunan dabi'a ta leken asiri.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng