Dan takarar kujeran gwamna a Gombe ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Dan takarar kujeran gwamna a karkashin Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe, Dr. Jamil Isyaku Gwamna ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) bayan zaben fidda gwani da aka yi a jiya.
Gwamna da wasu yan takara 7 sun fadi zaben fidda gwani na gwamna karkashin PDP a Gombe inda Sanata Bayero Nafada, sanata mai wakiltan Gombe ta arewa ya dare.
Bayan zaben fidda gwanin, Gwamna ya nuna rashin amincewa da sakamakon inda ya bayyana shirin a matsayin rashin adalci.

Asali: Depositphotos
Yayinda yake jawabi ga manema labarai a Gombe a ranar Talata, 2 ga watan Oktoba don sanar da sauya shekarsa, Gwamna yace barin PDP ba abu ne mai sauki ba kasancewa yana a jam’iyyar tun 2007 kuma ya zuba jari sosai da sadaukarwar da yayi wajen gina jam’iyyar a jihar.
KU KARANTA KUMA: Shugaban masu rinjaye a majalisa Lawan ya mallaki tikitin APC a Yobe
Yace bai sauya sheka don son zuciyarssa b assai dan ra’ayin mutanen dake tarayya dashi lokacin takarar sanna kuma don makomar mutanen Gombe.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.
Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Asali: Legit.ng