Zaben cikin gida: Mama Taraba ta lashe takarar kujerar gwamna a UDP

Zaben cikin gida: Mama Taraba ta lashe takarar kujerar gwamna a UDP

Tsohuwar Ministan Harkokin Mata da Ayyukan Cigaba, Aisha Alhassan wanda aka fi sani da Mama Taraba a ranar Laraba ta yi nasarar lashe tikitin takarar gwamna a karkashin jam'iyyar United Democratic Party UDP.

Mama Taraba ta lashe dukkan kuri'u 224 daga kananan hukumomi 16 da ke jihar a zaben da aka gudanar a Shield Hotel da ke Jalingo karkashin jagorancin Ciyaman din jam'iyyar na kasa,

A farkon makon nan ne dan takarar gwamna daya tilo a jam'iyyar, Abdulrazak Gidado ya sanar da cewar ya janyewa Mama Taraba.

Zaben cikin gida: Mama Taraba ta lashe takarar kujerar gwamna a UDP
Zaben cikin gida: Mama Taraba ta lashe takarar kujerar gwamna a UDP
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Dan Sule Lamido ya lashe takarar kujerar Sanata a PDP

Sai dai duk da hakan, dukkan wakilan jam'iyyar sun kafa kuri'unsu kafin aka tsayar da tsohuwar Ministan a matsayin wanda ta lashe tikitin takarar jam'iyyar a jihar.

Shugaban jam'iyyar na kasa, ya yabawa 'yan jam'iyyar sabbi da tsaffin saboda yada suka hada kawunansu waje guda wanda a cewarsa hakan zai karawa jam'iyyar damar samun nasara a jihar.

Okoye ya ce abubuwan alkhairi sun fara afkuwa a jam'iyyar tun lokacin da Mama Taraba da dumbin magoya bayanta suka shigo jam'iyyar.

A cikin 'yan kwanakin nan ne tsohuwar Ministan ta yi murabus daga mukaminta sannan ta fice daga jam'iyyar APC saboda jam'iyyar ta hana ta tikitin takarar gwamna bisa zargin ta da rashin cikakiyar da'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel