Wata mata tayi kukan neman taimako bayan ta haifi yan uku

Wata mata tayi kukan neman taimako bayan ta haifi yan uku

- Wata mata da Allah ya azurta da yan uku ta koka

- Tayi kira ga al’umman annabi da su kawo mata agaji domin ta samu damar kula da jariran

- A cewata mijinta na iya bakin kokarinsa amma bai da karfin rike yaran

Wata mata mai suna Malama Dausiyya Kabiru Ibrahim da Allah ya albarkata da haifar yan uku duk maza a kwanan nan tayi kira ga al’umman annabi da su kawo mata agaji domin ta samu damar kula da jariran.

Dausiyya wacce ke zaune a yankin Sheka na jihar Kano, ta haifi yan uku a asibitin Murtala Mohammed Specialist hospital.

Don haka ta roki masu kudi da su kawo mata tallafi ta hanyar daukar nauyin yaran, inda ta bayyana cewa “mijina mai kokari ne da kula da iyali amma bai da karfin daukar nauyin jariran da na Haifa."

Mahaifin yaran wanda ya kasance malamin Qur’ani, Malam Kabiru Ibrahim ya kuma roki jama’a da su agaza masu.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama barayin mota 3 a Kano

Yace ya gode ma Allah da wannan ni’ima da ya yi masa na bashi yara har uku a lokaci guda.

Yace baya ga koyarwa yana dan sana’ar hannu wanda daga ciki neyake kula da iyalinsa amma yanzu babu kasuwa inda rayuwa tayi masu wahala.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel