2019: Sanatoci 2 masu ci sun fadi zaben fidda gwani a wata jihar Arewa

2019: Sanatoci 2 masu ci sun fadi zaben fidda gwani a wata jihar Arewa

Biyu daga cikin sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dake mulki a jihar Niger sun fadi zaben fidda gwani a kokarinsu na ganin sun koma majalisar dokokin kasar a ranar Talata, 2 ga watan Satumba.

Sanatocin biyu sun sha kaye ne a zaben fidda gwani da aka gudanar a fadin yankuna uku na jihar.

A yankin Niger ta gabas, sanata da yayi mulki sau biyu kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan doka da yancin yan adam, David Umoru ya fadi inda sabon shiga, Sani Musa yayi nasara.

2019: Sanatoci 2 masu ci sun fadi zaben fidda gwani a wata jihar Arewa
2019: Sanatoci 2 masu ci sun fadi zaben fidda gwani a wata jihar Arewa
Asali: UGC

Haka zalika a yankin Niger ta arewa, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan bayanai, Sanata Aliyu Abdullahi ya fadi inda kwamishinan kananan hukumomi, ci gaba da harkokin shugabanni na jihar Niger, Zakari Jikantoro.

KU KARANTA KUMA: Kisan miji: Manyan lauyoyi 3 sun janye daga shari’ar Maryam Sanda

A Niger ta kudu, har yanzu ana nan ana kada kuri’a a lokacin wannan rahoton yayinda aka samu jinkiri wajen lokacin fara zaben saboda rashin zuwan kayayyakin zabe akan lokaci.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa da aka dai je da aka dawo, Sanata Dino Melaye zai sai sake takarar Sanata a zabe mai zuwa 2019 bayan ya lashe zaben fitar da gwani da aka ayi Jam’iyyar PDP.

Jam’iyyar PDP ta tsaida Dino Melaye a matsayin ‘Dan takarar ta na Majalisar Dattawa wanda zai wakilci Yankin Kogi ta Yamma a 2019. Babban Jami’in da ya gudanar da zaben fitar da gwanin watau Jude Sule ya tabbatar da wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel