Abubuwa sun cabewa wasu ‘Yan siyasa bayan Shehu Sani ya samu tikitin APC

Abubuwa sun cabewa wasu ‘Yan siyasa bayan Shehu Sani ya samu tikitin APC

Mun samu labari cewa jiya an ta ganin rikici iri-iri a cikin Garin Kaduna bayan da APC ta dauki tikitin Sanata ta mikawa Shehu Sani a sama. Uwar Jam’iyya ce dai ta dauki wannan mataki a jiya Talata.

2019: Abubuwa sun cabewa wasu ‘Yan siyasa bayan Shehu Sani ya samu tikitin APC
Sanatan Kaduna Shehu Sani ya samu tutan APC a bagas
Asali: Depositphotos

Daily Trust ta rahoto cewa Garin Kaduna ya yamutse bayan da labari ya iso gari cewa Jam’iyyar APC tayi watsi da sauran masu neman takaran Sanata a Yankin Kaduna ta tsakiya inda aka mikawa Sanata Shehu Sani tuta.

Yanzu haka dai Sanata Shehu Sani ne yake kan kujerar sai dai APC ta cire sunayen sauran mutane 3 da ke neman kujerar Sanatan daga cikin ‘Yan takara. Hakan ya sa wasu Magoya bayan APC su ka cika Gari da zanga-zanga.

Wasu ‘Yan APC ba su ji dadin wannan abu ba inda su kace Jam’iyya ta nuna masu fin karfi wajen kakaba masu ‘Dn takara daga Abuja. Sai dai wata Kungiya ta Kaduna Patriotic Front ta ji dadin wannan mataki da Jam’iyya ta dauka.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na hakura da takarar Sanata na bar ma Shekarau – Inji Lado

Hakan dai ya sa manyan Jami’an Gwamnatin Jihar sun yi zugum a Kaduna. Daga cikin masu neman kujerar akwai Masu ba Gwamna shawara Uba Sani da Lawal Sama’ila Yakawada da kuma Arc. Shamsuddeen Giwa.

Zangar-zangar dai sun ja har an tare manyan hanyoyi a cikin Gadin Kaduna inda Magoya Jam’iyyar da Sanatan su ke nuna mabanbantan ra’ayi. Har yanzu dai Gwamna Nasir El-Rufai wanda ba ya tare da Sanatan bai yi magana ba.

Kwanaki dai kun ji Sanatan na Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya bayyana yadda ya hana Jama’a saya masa fam din sake takara karkashin Jam’iyyar ta APC mai mulki a zabe mai zuwa na 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel