Babban abinda yasa na hakura da takarar Sanata na bar ma Shekarau – Inji Lado

Babban abinda yasa na hakura da takarar Sanata na bar ma Shekarau – Inji Lado

Guda daga cikin jigogin jam’iyyar APC reshen jahar Kano, kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya ya bayyana dalilin da yasa shi janyewa daga takarar daya kaddamar don komawa kujerarsa zaben 2019, kujerar da Kwankwaso ke kai a yanzu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Lado ya bayyana cewa babban abinda yasa shi janyewa daga takarar shine sabodan girman gwamnan jahar Kano, Abdullah Ganduje da yake gani, tare da kimarsa wanda ya daukeshi a matsayin uba a gareshi.

KU KARANTA: Sulhu alheri ne: An sasanta tsakanin yan takarar gwamna da zasu fafata a zaben fidda gwani a Zamfara

Babban abinda yasa na hakura da takarar Sanata na bar ma Shekarau – Inji Lado
Bashir Lado
Asali: Facebook

Cikin sanarwar da Lado ya fitar a ranar Talata 2 ga watan Oktoba, inda yace yana gode ma Gwamna Ganduje bisa shawarar daya bashi na janyewa daga takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya domin a kawar da ytiwuwar rikici a jam’iyyar APC musamman a yayin da ake tunkarar zabukan 2019.

“Baya ga janyewa daga takarar Sanatan Kano ta tsakiya, ina sanar da mika motocin yakin neman zabena guda ashirin da biyar da dukkanin wasu ofisoshin yakin neman zabena ga yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da sauran yan takarar mukamai daban daban.” Inji shi.

Daga karshe Sanata Bashir Lado yayi kira ga magoya bayansa dasu rungumi wannan matakin daya dauka da kyakkyawan zato, ba tare da nuna bacin rai ko wani abu makamancin haka ba.

Rahotanni sun watsu a baya na cewa Sanata Lado ya janye takararsa ne ga tsohon gwamnan jahar Kano, Malam Ibrahim Shekarau wanda a yanzu shine a gaba gaba a cikin yan takarkarun dake muradin darewa kujerar da Kwankwaso ya yi dare dare akai, musamman duba da Kwankwaso ba zai sake neman kujerar ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel