Gaya da Sumaila sun sa hannu a wata yarjejeniya a gaban ‘Yan Sanda

Gaya da Sumaila sun sa hannu a wata yarjejeniya a gaban ‘Yan Sanda

Mun samu labari cewa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da Honarabul Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila sun sa hannu a wata yarjejeniya a gaban ‘Yan Sanda domin kauda rikici a siyasar Kano a zabe na 2019.

Gaya da Sumaila sun sa hannu a wata yarjejeniya a gaban ‘Yan Sanda
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya yana neman komawa kujerar sa
Asali: Twitter

Sanatan Kano ta Kudu Kabiru Gaya sun zauna Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin Majalisar Wakilai watau Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila inda su kayi alkawarin cewa ba za su tada hatsaniya a zabe ba.

Kwanan nan ne za ayi zaben fitar da gwani na takarar kujerar Sanatoci sai dai da alamu Jam’iyyar APC ta dage zabukan. Kabiru Gaya da Kawu Sumaila su na neman takarar kujerar Sanatan Kano ta Kudu a karkashin Jam’iyyar APC.

KU KARANTA: 'Yan siyasan da su kayi batan baka-tan-tan a PDP

Manyan ‘Yan siyasan sun zauna tare da Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda da DSS da kuma Jami’an NSCDC inda su ka sa hannu cewa za ayi siyasa ba tare da gaba ba a Garin Kano. A baya ma dai an taba yin irin wannan yarjejeniya a Jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano Rabi’u Yusuf yace Gaya da Sumaila sun yi alkawarin cewa za su ja hankalin Magoya bayan su wajen ganin babu wanda ya tada rikici a wajen zaben na fitar da gwani na Jam’iyyar APC mai mulki.

A baya dai an samu rigima wajen kamfe inda har aka yi wa Jama’a barna a Yankin na Kano ta Kudu don haka wannan karo aka nemi ayi siyasar cikin tsabta. Kawu Sumaila wanda ya taba yin ‘Dan Majalisa yana harin kujerar Sanata yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel