Sulhu alheri ne: An sasanta tsakanin yan takarar gwamna da zasu fafata a zaben fidda gwani a Zamfara

Sulhu alheri ne: An sasanta tsakanin yan takarar gwamna da zasu fafata a zaben fidda gwani a Zamfara

Daga karshe rikicin cikin gida daya dabaibaye jam’iyyar APC reshen jahar Zamfara yazo karshe bayan an sanya ranakun gudanar da zaben fitar da gwanin da zai tsaya mata takarar gwamna har sau uku, amma kuma ana dagewa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu haka an sanya ranar yau Laraba, 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za’a gudanar da zaben, ba kamar yadda gwamnan jahar yace an dage zaben ba har sai baba ta ji.

KU KARANTA: Wuta ta babbaka ofisoshin malamai 30 da sakamakon jarabawar dalibai a kwalejin kimiyya da fasaha

Shugaban kwamitin shirya zaben, Dakta Abubakar Fari ne ya tabbatar da wannan cigaban, inda yace matsalar dake tsakanin bangaren gwamnan jahar Abdul Aziz Yari da bangaren yan adawar gwamnan da suka kunshi gagga gaggan yan siyasa kuma yan takara su takwas a yanzu ta kau.

“Mun warware dukkan matsalolin dake son dabaibaye zaben da muke shirin gudanarwa, don haka za’a fara gudanar da zaben daga safiyar Laraba a dukkanin mazabun dake fadin jahar Zamfara.” Inji shi.

Takaddama ta kunno kai ne a cikin jam’iyyar APC ta jahar Zamfara ne sakamakon tuburewa da gwamnan jahar Abdul Azii Yari yayi akan lallai kwamishinan kudi na jahar, Alhaji Mukhtar Idris ne kadai ya cancanci zama gwamna, yayin da mataimakin gwamna Ibrahim Wakkala da wasu yan siyasa takwas dake ganin ba zata sabu ba wai harba bindiga a ruwa, suka ja daga da shi.

Daga cikin yan takarar gwamnan su takwas dake adawa da Yari akwai Mataimakin gwamna Ibrahim Wakkala, ministan tsaro Mansur Dan Ali, Sanata Kabiru Marafa, tsohon gwamna Mahmud Aliyu Shinkafi, dan majalisa Aminu Sani Jaji, Engineer Abu Magaji, Dauda Lawal da Mohammed Sagir Hamid.

Zamu zuba idanu don ganin yadda za ta kaya a wannan zabe mai cike da sarkakiya domin tabbatar da ingancin batun da shugaban kwamitin shirya zaben Dakta Fari yayi ko akasin haka, da fatan ayi taro lafiya, yan kallo lafiya yan wasa ma lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel