ASUU ta gargadi al'umma kan karin kudin makaranta da gwamnati ke shirin yi

ASUU ta gargadi al'umma kan karin kudin makaranta da gwamnati ke shirin yi

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU ta janyo hankalin al'umma kan wata yunkurin da gwamnatin tarayya keyi na kara kudin makarantun daliban jami'a zuwa N350,000 duk shekara.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Zonal Chairman din kungiyar, Dr Ade Adejumo yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Ibadan inda ya ce tawagar gwamnatin tarayya karkashin kagorancin Dr Wale Babalakin ne suka sanar dashi yayin da suka ziyarci kungiyar a Ibadan.

Ya yi kira da 'yan Najeriya su hada karfi da karfe da kungiyar domin ganin cewa gwamnatin ta dauki matakan habbaka karatu a jami'o'in gwamnati

ASUU ta gargadi mutane kan karin kudin da gwamnati ke shiryawa
ASUU ta gargadi mutane kan karin kudin da gwamnati ke shiryawa
Asali: Facebook

.DUBA WANNAN: Mata ta da Buhari ne kadai masu gidana a duniya - gwamnan PDP

Ciyaman din ya nuna rashin goyon bayansa ga shirin da gwamnati keyi na kafa bankin bawa dalibai bashi domin biyan kudin makaranta sai dai ya yi kira ga al'umma su sake duba kan lamarin domin samun masalaha.

Kungiyar kuma tayi kira ga gwamnatin tarayya ta cika mata alkawurran da suke cikin yarjejeniyar da ASUU da gwamnati suka rattaba hannu a shekarar 2017 idan kuma ba hakan ba akwai yiwuwar kungiyar ta shiga yajin aiki.

Kazalika, kungiyar ta ce babu kanshin gaskiya cikin ikirarin da gwamnati tayi na cewa ta bawa kungiyar N20 biliyan domin a cewarsu makarantu aka bawa kudaden ba kungiyar ASUU ba. Ta ce abin dariya ne gwamnatin tayi alfahari da bawa jami'o'i 64 N20 biliyan domin ya yi kadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel