Waka a bakin mai ita: Tinubu ya bayyana dalilinsa na juyawa Ambode baya

Waka a bakin mai ita: Tinubu ya bayyana dalilinsa na juyawa Ambode baya

- Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana dalilin da yasa ya daina goyon bayan gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode

- Wannnan shine karo na farko da Tinubu ya yi magana a kan harkallar siyasar da ta saka shi juyawa Ambode baya

- An dade ana ta hasashen dalilan da suka jawo lalacewar dangantaka tsakanin Ambode da maigidansa Tinubu

A yau, Talata, 2 ga watan Oktoba, ne jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya bayyana dalilinsa na daina goyon bayan gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode, a kokarinsa na sake komawa karagar mulki a karo na biyu.

Da yake magana da manema labarai a mazaba ta "C" dake Ikeja a garin Legas, Tinubu, ya ce Ambode ya yi kokari a matsayinsa na gwamna sai dai bashi da halil irin na 'yan siyasa.

Tinubu ya kara da cewar shi ma tilas ya zame masa ya ajiye Ambode saboda haka magoya bayan jam'iyyar APC a jihar Legas ke bukata.

Waka a bakin mai ita: Tinubu ya bayyana dalilinsa na juyawa Ambode baya
Tinubu da Ambode
Asali: Depositphotos

Da yake amsa tambayar dalilin da yasa ya baya goyon bayan takarar Ambode, Tinubu ya ce: "wanne dan takara na goyawa baya a shekarar 2014? kuma kun san Ambode ne. Duniya juyi-juyi ce. Mutanen da suka mayar da ni shugaba ne a Legas suka bukaci mu canja dan takara, ba wai ra'ayi na bane.

"Idan har zan zama shugaba ko jagora nagari, to tabbas na bi zabinsu ko kuma nima su daina goya min baya. Kun ga kenan daina goyon bayan Ambode abu ne da nima ya fi karfi na," a kalaman Tinubu.

DUBA WANNAN: Tura ta kai bango: Ambode ya tonawa dan takarar Tinubu asiri

Kazalika tsohon gwamnan ya bayyana cewar Ambode ya yi kokarin ta fuskar aiyukan raya kasa a Legas, sai dai ya ce bashi da hali irin na 'yan siyasa kuma hakan kan iya jawowa jam'iyyar APC asarar magoya baya.

Tinubu ya bayyana cewar rashin samun takarar Ambode ba zai shafi farinjini ko kuri'un da jam'iyyar APC zata samu a jihar Legas ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel