Da dumi-dumi: PDP tayi zaben fiida gwaninta a gidan Kwankwaso cikin dare

Da dumi-dumi: PDP tayi zaben fiida gwaninta a gidan Kwankwaso cikin dare

Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na jihar Kano ta gudanar da zaben fitar da gwanin kujerar gwamnan jihar a gidan babban jigon jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

An kaddamar da zaben ne misalin karfe 12 na dare game da rahoton da jaridar Daily Nigerian ta samu.

A ranan Litinin, jami’an yan sandan sun hana yan jam’iyyar gudanar da zaben fitar da gwanin a Marhaba Cinema, inda aka shirya gudanar da zaben sakamakon umurnin kotu.

Majiya mai karfi ya bayyana cewa deleget mabiya Kwankwasiyya Surukiyya kadai aka amince su yu musharaka cikin zaben fidda gwanin.

KU KARANTA: 2019: Fintiri ya lashe zaben fidda gwani a jihar Adamawa

Ga dukkan alama, surukin Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf, ne zai zama gwanin zaben tunda babu alaman wasu yan takara irinsu tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafiz Abubakar a wajen.

Amma daga baya, an samu rahoton cewa dan takara guda kadai wanda ba kan Kwankwasiyya da aka gani a wajen shine Jafar Sani Bello.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel