2019: Usani Usani zai nemi Gwamnan Jihar Kuros Riba a Jam'iyyar APC

2019: Usani Usani zai nemi Gwamnan Jihar Kuros Riba a Jam'iyyar APC

Mun samu labari dazu cewa Ministan harkokin Neja-Delta watau Fasto Usani Usani Uguru zai nemi kujerar Gwamnan Jihar Kuros Riba a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki a zabe mai zuwa.

2019: Usani Usani zai nemi Gwamnan Jihar Kuros Riba a Jam'iyyar APC
Ministan Neja Delta zai nemi takarar Gwamna a 2019
Asali: UGC

Fasto Usani Usani ne yayi nasarar lashe tikitin APC a zaben fitar da gwani na Jam’iyyar mai mulki. Shugaban harkar zaben Gwamnan a APC na Jihar Emmanuel Anom ya sanar da sakamakon zaben da aka yi a babban Garin Kalaba.

Useni Uguru ya samu kuri’u 47,313 a zaben inda Sanata Owan Enoh ya tashi da kuri’u 14, 860. Haka-zalika Farfesa Eyo Etim Nyong ya tashi da kuri’u 1,162. John Odey da kuma Cif Edem Duke sun samu kuri’u 1,099 da kuma 1,322.

KU KARANTA: Ogboru ya lashe zaben fidda gwani na gwamna a Jihar Delta

Ministan yayi nasara ne a kowace Karamar Hukuma 18 na Jihar. Sai dai wasu ‘Yan taware a Jam’iyyar sun yi wani zaben dabam inda su ka tsaida na su ‘Yan takarar. Ba mamaki Ministan yanzu zai yi murabus daga kujerar sa.

Jam’iyyar APC dai za ta kara ne da PDP mai mulki a Jihar inda Gwamna Ben Ayade zai nemi tazarce. A baya dai kun ji cewa Ministar harkokin mata Aisha Alhassan ta yi murabus sannan kuma ta fice daga APC inda tayi niyyar takara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel