Takarar gwamna: Nuhu Ribadu ya yi amai ya lashe game da zaben fidda gwani
Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya yi amai ya lashe tare da tafka mi’ara koma baya game da zaben fitar da gwanin takarar gwamnan jahar Adamawa na jam’iyyar APC, kamar yadda jaridar TheCables ta ruwaito.
Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar Lahadi 30 ga watan Satumba ne Malam Nuhu ya sanar da janyewa daga takararsa ta gwamnan jahar Adamawa sakamakon rashin adalcin da yayi zargin an tafka a zaben fitar da gwani na jam’iyyar da aka yi a jahar.
KU KARANTA: An kashe wani matashi da nuna farin cikinsa da kisan da yan ta’adda suka yi ma janar Alkali a garin Jos
Sai kwatsam aka jiyo tsohon shugaban na EFCC ya sanar da janye wancan maganan da yayi na janye takararsa, inda yace ya dauki wannan sabon matakin sakamakon matakin soke zaben da aka gudanar da uwar jam’iyyar APC ta yi ne.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito daraktan yakin neman zaben Nuhu Ribadu, Salihu Bawuro ne ya sanar da haka a ranar Litinin 1 ga watan Oktoba ga manema labaru a garin Yola, babban birnin jahar Adamawa.
Bawuro yace cibiyar yakin neman zaben dan takarar gwamnan jahar Adamawa a karkashin jam’iyyar APC, Nuhu Ribadu ta gamsu da matakin da uwar jam’iyyar APC ta dauka na soke zaben fitar da gwani da aka ce an shirya a garin Yola, sa’annan ta sanya ranar da za’a sake gudanar da sahihin zabe.
“A yanzu da uwar jam’iyya ta shiga cikin magana zaben da ake ikirari an gudanar a ranar lahadi da nufin gyara matsalolin da aka samu, Malam Nuhu Ribadu ya janye batun ficewa daga takara, kuma ya dawo da karfinsa don ganin ya samu nasara a zaben da za’a sake yin a kato bayan kato.” Inji shi.
Daga karshe Bawuro a shirye suke su fafata a wannan zabe, sa’annan yace zasu yi dukkan mai yiwuwa don ganin zaben ya gudana cikin gaskiya da adalci. uwar jam’iyyar APC ta sanya ranar Alhamis 4 ga watan Oktoba a matsayin ranar da zata gudanar da sabon zaben fitar da gwani na APC a Adamawa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa
Asali: Legit.ng