Gwamnan jahar Kaduna ya sha ruwan kuri’u a zaben fitar da gwani na APC

Gwamnan jahar Kaduna ya sha ruwan kuri’u a zaben fitar da gwani na APC

Jimillan yayan jam’iyyar APC kuma wakilan da suka kada ma gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai kuri’u a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC na takarar gwamnan jahar, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Lahadi, 30 ga watan satumba ne aka gudanar da wannan zabe a dandanlin Murtala dake garin Kaduna, inda wakilai dubu uku da dari bakwai da tamanin da biyu (3, 782) daga kananan hukumomi ashirin da uku suka kada kuri’a.

KU KARANTA: Rikicin siyasar Kano ya dauki sabon salo yayin da PDP zata fitar da takarar gwamna a yau

Shugaban zaben, Mathew Idukriyekemwen ya tabbatar da nasarar Gwamna El-Rufai, inda yace gwamnan ya samu kuri’a 2447, yayin da aka samu gurbatattun kuri’u taaktin da uku (33), sai dai shugaban zaben bai bayyana matsayin kuri’u dubu daya da dari uku da biyu (1,302) da suka rage ba.

Gwamnan jahar Kaduna ya sha ruwan kuri’u a zaben fitar na gwani na APC
Gwamnan jahar Kaduna
Asali: Facebook

Daga karshe shugaban zaben Iduoriyekemwen ya bayyana godiyarsa ga yadda aka gudanar da zaben cikin lafiya da kwanciyar hankali, shima a nasa jawabin, gwamnan jahar Kaduna Malam El-Rufai ya gode ma yayan jam’iyyar da suka gamsu da kamun ludayinsa.

“Na amince da wannan amana da jam’iyyarmu ta bani na tsayawa takarar gwamnan jahar Kaduna, na daukeshi a matsayin kira gareni da na cigaba da ayyukan da muke yin a farfado da martabar jahar Kaduna, kuma mun dukufa wajen ciyar da talakawa gaba.” Inji shi.

Daga karshe gwamnan yayi kira ga yayan jam’iyyar APC dasu hada kawunansu don tabbatar da nasarar jam’iyyar a zabukan 2019 tun daga sama har kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel