Cikin Hotuna: Shugaban hafsin sojin sama ya je mika ta'aziyya ga Mahaifan Sojan Saman nan da Ajali ya katsewa hanzari
Mun samu cewa a ranar yau ta Asabar ne shugaban hafsin sojin sama na Najeriya, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, ya kai ziyarar mika ta'aziyya ga Mahaifan Marigayi Muhammad Bello Baba-Ari, sojan saman nan da ajali ya katsewa hanzari.
Rayuwar Marigayi Baba Ari ta zo karshe yayin da ya yi gamo da ajali a sanadiyar hatsarin jirgin sama da ya auku cikin jihar Kaduna a ranar Asabar din gabata.
Tawagar shugaban hafsin sojin saman ta hadar da manyan dakaru 10 na rassan hukumar sojin daban-daban, inda suka mika ta'aziyyarsu ga Mahaifinsa, Alhaji Abu Baba-Ari.

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC
KARANTA KUMA: Boko Haram sun salwantar da rayukan Mutane 6 a gabar Tafkin Chadi
Shugaban hafsin sojin saman ya bayyana Marigayi Baba-Ari a matsayin jami'in ta mai kwazon gaske da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yiwa kasar sa ta Najeriya hidima tare da muhimmiyar rawar gani da ya taka wajen bayar da gudunmuwa ta yakar ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.
Kazalika tawagar ta kai ziyara ta dubiya ga sauran sojin biyu da kwanan su ke gaba yayin da aukuwar hastarin jirgin saman ta hadar da su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng