Boko Haram sun salwantar da rayukan Mutane 6 a gabar Tafkin Chadi

Boko Haram sun salwantar da rayukan Mutane 6 a gabar Tafkin Chadi

Kamar yadda rahotanni da sanadin hukumomin tsaro suka bayyana a ranar Asabar ta yau, kimanin rayukan Mutane 6 ne suka salwanta da suka hadar har da soji biyu a wani sabon harin Boko Haram da ya afku a gabar tafkin Chadi.

Majiyar rahoton ta dakarun sojin kasa kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito ta bayyana cewa, dakarun sojin kasar Chadi sun mayar da martani cikin gaggawa inda suka samu nasarar salwantar da rayukan 'yan ta'adda 17 a gabar Tafkin.

Rayukan jami'ai uku masu sintiri a dokar daji, ma'aikatan hukumar hana fasakauri biyu da kuma dakarun soji biyu sun salwanta a yayin wannan hari da ya auku a garuruwan Moussaroum da kuma Ngueleya dake yankin Kudu na gabar Tafkin Chadi.

Kakakin hukumar sojin kasar Chadi, Kanal Azam, shine ya bayar da tabbacin aukuwar wannan mummunan lamari yayin ganawarsa da manema labarai na jaridar AFP.

Boko Haram sun salwantar da rayukan Mutane 6 a gabar Tafkin Chadi
Boko Haram sun salwantar da rayukan Mutane 6 a gabar Tafkin Chadi
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, harin Boko Haram na karshe a gabar Tafkin ya auku ne a ranar 22 ga watan Yulin da ta gabata, inda ya salwantar da rayukan mutane 18 daura da kauyen Daboua dake kan iyaka ta Kasar Nijar.

KARANTA KUMA: Boko Haram ta kashe wani Kwamandan ta da ya yi yunkurin mika wuya

A halin yanzu rayukan kimanin Mutane 20, 000 sun salwanta tare da raba kimanin Mutane 2m da muhallan su a gabar Tafkin tun yayin da Kungiyar ta fantsama cikin zartar da ta'addanci a shekarar 2009 da ta gabata.

Legit.ng ta ruwaito cewa, dakarun kasashen Chadi, Kamaru da kuma Nijar sun hada gwiwa da dakarun sojin Najeriya domin yakar ta'addancin kungiyar Boko Haram da ta ki ta ki cinyewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel