Kamfunnan Sadarwa sun jawo wa gwamnati asarar tiriliyan daya ta Nairori - NCC

Kamfunnan Sadarwa sun jawo wa gwamnati asarar tiriliyan daya ta Nairori - NCC

- Akwai babbar kasuwar sadarwa a Najeriya

- An tafka asarar N1T a cikin shekaru biyu kacal

- Akwai masu amfani da wayar salula 120m a Najeriya

Kamfunnan Sadarwa sun tafka asarar tiriliyan daya ta Nairori - NCC
Kamfunnan Sadarwa sun tafka asarar tiriliyan daya ta Nairori - NCC
Asali: Depositphotos

Shugaban hukumar NCC, ta bakin mai magana da yawunsa, Felicia Onwuegbuchulam, daraktar hukumar ta fannin kula da masu amfani da layukan sadarwa, yace gwamnati da kamfunnan sadarwa sun janwo wa NAjeriya babbar asara.

A cewarsa, kamfunnan, sun komasatar hanya don kin nuna kiran da ake yi daga kasashen waje, inda sukan boye lambar su basu lambarr cikin gida.

A cewarta, boye lambar, yana hana a caji kira N24, maimakon N3 da ake cira a kiran cikin gida.

DUBA WANNAN: Sai na zarce zaku san me ake kira aiki - Buhari

Ta ce, an gano irin wadannan lambobi har 750,000 cikin shekaru biyu, kuma an toshe su daga aiki, sannan hukumar tayi kira da a kula a dinga bada rahoton irin wadannan lambobi don magance cuwa-cuwas da ake wa gwamnati.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel