'Munafuncin dare' ya sa muka ware Mama Taraba daga takarar gwamna - Oshiomhole

'Munafuncin dare' ya sa muka ware Mama Taraba daga takarar gwamna - Oshiomhole

- Mama Taraba, yar jam'iyyar APC da rana, da dare kuma yar PDP

- Jam'iyyar APC ta zargi ministan harkokin mata da cin amanar jam'iyyar ta bayan fage

- Rashin cancantar ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya biyo bayan rashin yin bautar kasa

'Munafuncin dare' ya sa muka ware Mama Taraba daga takarar gwamna - Oshiomhole
'Munafuncin dare' ya sa muka ware Mama Taraba daga takarar gwamna - Oshiomhole
Asali: Depositphotos

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana yanda jam'iyyar ta ke zargin ministan harkokin mata, Hajiya Jumai Alhassan, da cin amanar jam'iyyar ta bayan fage, misalta da yar jam'iyyar APC da rana kuma yar PDP da dare.

Ya fadi hakan ne a taron manema labarai na ranar juma'a a Abuja.

Oshiomhole ya bada dalilin da jam'iyyar ta kakkabo ministan sadarwa Adebayo Shittu, saboda kin yin bautar kasa wanda hakan ya dasa ayar tambaya akan tarbiya da shari'a.

DUBA WANNAN: Mama Taraba ta bar APC

"Shittu da kanshi ya tabbata bai yi wajibtacciyar bautar kasa da dokar Najeriya ta yanke ba. A hukuncin shi, Dan majalisar jiha da yayi da kuma ministan tarayya, yayi su ne saboda jajircewar shi ne. Amma mu jam'iyyar mu ta San bautar kasa dole ne. Ba abinda Dan kasa ke da zabin yi ko kin yi bane." inji Oshiomhole

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel