Abin boye ya fito: Sirrukan sabon gwamnan Osun, Oyetola, da baku sani ba

Abin boye ya fito: Sirrukan sabon gwamnan Osun, Oyetola, da baku sani ba

- An gano ashe akwai dangantakar jini tsakanin zababen gwamnan Osun, Gboyega Oyetola da Bola Tinubu

- Wasu bayanan kuma sun nuna cewa Oyetola ne ke tafiyar da lamuran gwamnatin jihar Osun a matsayinsa na shugaban ma'aikatan jihar

- An kume ce akwai kyakyawar alakar aminta tsakanin Asiwaju Bola Tinubu ta Gboyega Oyetola

Wani abin mamaki game da Gboyega Oyetola shine bai taba takarar zabe a baya ba duk da ya dade ana damawa da shi a harkokin siyasa. An kuma ce shine ke juya akalar mulkin gwamna mai barin gado Rauf Aregbesola tunda shine shugaban ma'aikata na gwamnatin jihar.

An gano dangatakar da ke tsakanin Oyetola da Tinubu
An gano dangatakar da ke tsakanin Oyetola da Tinubu
Asali: Depositphotos

Babban abinda mutane ba su sani ba a kan Oyetola shine dangatakar da ke tsakaninsa da Shugaban APC, Bola Ahmed Tinubu, an gano cewa mahaifiyar Tinubu da mahaifin Oyetola duk mahaifinsu guda. Hakan ke nuna wa da kani su ke.

DUBA WANNAN: Zaben Osun: Yarjejeniyar da muka kula da Omisore - Oshiomhole

Baya ga haka, Oyetola yana daya daga cikin mutanen da Tinubu ya amince da su. Haka yasa ba abin mamaki bane yadda Asiwaju Tinubu ya tare a Osogbo na dan wasu kwanaki domin ya tabbatar kaninsa ya yi nasarar lashe zaben.

Duk da irin takadamar da ake yi game da sakamakon zaben, Oyetola ya kafa tarihi na lashe zabe a jihar wadda ake ganin zai mulke ta cikin sauki saboda kwarewa da gogewa da ya samu a matsayinsa ma shugaban ma'aikatan jihar na tsawon shekaru 8.

An haifi shi ne ranar 29 ga watan Satumban 1954 a Iragbiji da ke karamar hukumar Boripe a jihar ta Osun. Ya yi karatun digirinsa ta farko da digiri ta biyu a Jami'an Legas a fanin Inshora da kasuwanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel