2019: Yadda zaben fitar da gwanin takarar shugabancin kasa a APC ta kasance a Jigawa

2019: Yadda zaben fitar da gwanin takarar shugabancin kasa a APC ta kasance a Jigawa

- An gudanar da zaben fitar da gwani na takarar shugabancin kasa ta APC cikin kwanciyar hankali a Jigawa

- An ruwaito cewar mutane da dama sun fita kwan su da kwarkwata domin kada kuri'unsu a mazabu daban-daban

- Tuni dai an fara kidayar kuri'un da mambobin suka kada a hedkwatan kananan hukumomin daban-daban da ke jihar

Mun samu daga Daily Trust cewa a yau Juma'a mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ke jihar Jigawa sun gudanar da zaben fitar da gwani da takarar shugabancin kasa a jam'iyyar cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Rahoton da majiyar Legit.ng ta bayyana cewa an tantance 'yan jam'iyyar da Katchi, Limawa da Jigawan Tsada ta hanyar nuna katunnan zama 'yan jam'iyya kana daga bisani suka kada kuri'unsu lami-lafiya.

2019: Yadda zaben fitar da gwani na takarar shugabancin kasa a APC ta kasance a Jigawa
2019: Yadda zaben fitar da gwani na takarar shugabancin kasa a APC ta kasance a Jigawa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Fitar da 'yan takara: APC ta nada gwamnoni a matsayin jami'an zabe

Majiyar ta ce mutane sun fito kwan su da kwarkwata domin an gano misalin mutane 300 a kan layi suna jiran su kada kuri'unsu a wasu rumfunan kada zaben da rana misalin karfe 2.30.

Kazalika, Daily Trust ta ruwaito cewa an gudanar za zabukan fitar da gwanin a yankin Hadejia cikin kwanciyar hankali kuma mutane sunyi tururuwa zuwa wajen kada kuri'unsu.

Tuni dai an fara kidayar kuri'un da mambobin suka kada a hedkwatan kananan hukumomin daban-daban da ke jihar.

A baya Legit.ng ta kawo muku cewa an samu jinkirin fara zaben fitar da gwanin na shugabancin kasa a jihar Nasarawa inda har misalin karfe 2.00 na rana galibin wuraren kada kuri'un suke wayam.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel