Jadawalin Zaben fidda Gwanayen takara na jam'iyyar APC
A yayin da a yau muka kawo ma ku rahoton cewa jam'iyyar APC ta sauya ranar gudanar da zaben fidda gwanaye manema tikitin takarar kujerun gwamnoni na jihohin kasar nan, mun kuma kawo jadawalin zaben fidda gwanaye na sauran manyan kujeru.
Rahotanni sun bayyana cewa, shugabannin jam'iyyar sun dage ranar gudanar da zaben fidda gwanayen takarar kujerun gwamnoni na jihohin kasar nan zuwa ranar Lahadi da ta yi daidai da ranar 30 ga watan Satumba sabanin ranar Asabar 29 ga watan na Satumba da ta kayyade a baya.
Mukaddashin Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Mista Yekini Nabena, shine ya bayyana wannan lamari na sauyin ranar gudanar da zaben cikin wata sanarwa a ranar Alhamis din da ta gabata.
A sanadiyar haka jaridar Legit.ng ta kawo muku jadawalin gudanar da zaben fidda gwanayen takarar manyan kujeru na kasar nan a karkashin jam'iyyar ta APC kamar haka:
Zaben fidda gwanayen takara na Majalisar dattawa - Ranar Talata, 2 ga watan Oktoba, 2018.
Zaben fidda gwanayen takara na Majalisar Wakilai - Ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba, 2018.
Zaben fidda gwanayen takara na Majalisun dokoki na jihohin kasar nan - Ranar Alhamis 4 ga watan Oktoba, 2018.
KARANTA KUMA: 2019: 'Dan Uwan Aisha Buhari ya kulla yarjejeniya da Nuhu Ribadu kan takarar Kujerar Gwamnan jihar Adamawa
Sai kuma ranar Asabar 6 ga watan Oktoba da za a gudanar da gangamin jam'iyyar inda za a fidda gwanin takarar kujerar shugaban kasa.
Legit.ng ta kuma fahimci cewa, ba bu wani manemin takarar kujerar shugaban kasa da jam'iyyar za ta tsayar face shugaban kasa Muhammadu Buhari, kasancewar sa dan takara daya tilo da tuni ya mallaki fam dinsa na bayyana kudirin takara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng