Wutar lantarki tayi qasa a kasa baki daya, ta dawo megawatt 3,700 kacal

Wutar lantarki tayi qasa a kasa baki daya, ta dawo megawatt 3,700 kacal

- Wutar lantarki tayi kasa a kasar nan a lokacin da ake tsaka da yajin aiki

- Kamfunnan sayar da wutar sun tafka asarar N381b

- Alkawurran da APC ta dauka a 2015 akwai batun samar da wuta kullum

Wutar lantarki tayi qasa a kasa baki daya, ta dawo megawatt 3,700 kacal
Wutar lantarki tayi qasa a kasa baki daya, ta dawo megawatt 3,700 kacal
Asali: UGC

Tashoshin dake samar da wutar lantarki wadanda aka kafa tun lokacin Obasanjo, wanda ake kira GenCos karkashin shirin NIPP, yanzu dai sun sanar da cewa wutar lantarki tayi kasa warwas, inda daga Megawatt 5,222 da ake iya samar wa, aka koma samar da 3,761 kacal.

Matsalolin da suka haifar da hakan, a cewar ministan wuta da makamashi Raji Fashola, yace sun hada da rashin iskar gas, tsufan kayan aiki, kasawar kamfunnan saboda kin biyansu kudin wuta da jama'a kanyi.

Ya kuma ce daminar bana ma ta kawo cikas saboda ambaliya da uban ruwa da yasha kan injinan aikin sarrafa wutar ta lantarki.

DUBA WANNAN: Rikici a Jos ya hallaka 14

Sai kuma batun kudaden da suke iya samu, inda rahoton ya nuna sun tafka babbar asara ta kudi da ta kai akalla N381b, kudan dala biliyan daya kenan a tsakanin nan.

An dai sayar da tsohuwar NEPA ne don a samu a zamanantar da harkar lantarkin saboda masu zuba jari su iya zuwa su tafikar da ita tamkar yadda aka yi da NITEL da Nigeria Airways, sai dai har yanzu sashen na fuskantar matsaloli da basu rasa nasaba da 'kasuwanci da tsari irin na kasashenmu na Afirka'

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel