'Yan kwagila masu shgo da mai sunce gwamnatin Tarayya tayi hobbasa ta biya su bashin N650b

'Yan kwagila masu shgo da mai sunce gwamnatin Tarayya tayi hobbasa ta biya su bashin N650b

- Muna bin Gwamnatin tarayya Naira biliyan 650 na tallafin mai

- Biyan bashin zai iya kare kadarorin mu daga zama gwanjon bankuna

- Duk da dai gwamnati tayi alkawarin biyan bashin, amma har yanzu shiru

'Yan kwagila masu shgo da mai sunce gwamnatin Tarayya tayi hobbasa ta biya su bashin N650b
'Yan kwagila masu shgo da mai sunce gwamnatin Tarayya tayi hobbasa ta biya su bashin N650b
Asali: Facebook

Kungiyoyin yan kasuwar man fetur ta Najeriya masu zaman kansu, sun koka akan bashin da suke bin Gwamnatin tarayya na tallafin kudin mai har Naira biliyan 650,inda suka ce biyan bashin zai iya tserar da dukiyoyin su.

A tattaunawa dasu da akayi, yan kasuwar man sun bayyana cewa biyan su bashin zai tserar da kadarorin su daga zama gwanjon bankuna.

DUBA WANNAN: Rikici a Jos ya kashe akalla mutum 14

Zababben sakataren kungiyar DAPPMA, Mista Olufemi Adewole ya bukaci gwamnati da ta rage hanyoyin da kudin zasu bi kafin su iso musu, gani da cewa bashin ya kawo rasa aiyukan mutane da dama a masana'antar mai da iskar gas.

Yace kashi 60 cikin dari na yan kasuwar sun bar kasuwancin saboda bankuna su karbe guraren su da sauran hannayen jarin su sakamakon kin maida bashin da sukayi.

Kamar yanda yace, da yawa kuma ana ta fafutukar cigaba da sana'ar duk da barazanar da suke samu a wasu bangarori.

DAPPMA tace Gwamnatin tace tana ta shirye shiryen biyan su amma har yanzu shiru kake ji don ko sisi bai iso ga yan kasuwar ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel