Rigimar daren jiya a Filato ta kar mutane har zuwa yinin nan na Juma'a, 14 sun rasu
- Akwai yuwuwar rasa rayukan mutane da dama a titin Rukuba, kusa da garin Jos
- Yan bindiga dadi sukayi dirar mikiya a yankin cikin dare inda suka halaka mutane goma
- Matasa suka tashi a yau domin daukar fansa

Asali: Depositphotos
Akwai yuwuwar rasa rayukan mutane da dama a titin Rukuba dake kusa da garin Jos domin an kai hari a yankin a ranar Alhamis da dare wanda hakan yasa masu daukar fansa suka kashe ma wadanda basu ba, basu gani ba a safarar juma'a.
Majiyar mu ta sanar damu cewa yan bindiga dadi ne sukayi dirar mikiya a yankin da dare lokacin ana ruwa, inda suka kashe mutane 10.
Matasan yankin suka tashi daukar fansa inda suka tare masu ababen hawa suka dinga kashewa. Babu tabbacin mutane nawa matasan suka dau fansa akai.
Amma jami'in yada labarai na 'Operation Safe Haven' Major Adam Umar da jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sanda, DSP Tyopev Terna yace jami'an tsaro na gurin a halin yanzu.
Majiyar mu dai ta kasa shaguna duk a rurrufe suke a yankin.
DUBA WANNAN: Yadda ake kidayar hatsi a kimiyya
Karin bayani: Yanzu haka an tabbatarcewa akalla mutum 14 ne suka rasa rayukansu a hatsaniyar - daga Channels TV.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng