Suna kirana 'Baba Go Slow' amma yanzu ina masu hanzarin su ke? - Shugaban kasa Buhari

Suna kirana 'Baba Go Slow' amma yanzu ina masu hanzarin su ke? - Shugaban kasa Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana da tabbacin cewa mata masu nakuda za su fito su zabe shi a 2019

- Shugaban kasar ya ce idan har aka sake bashi dama a 2019, zai tabbatar ya kara kaimi akan wanda ya nuna yanzu

- Buhari ya ce masu adawa sun dade suna kiransa da 'Baba Go Slow', to amma wadanda ke tafiya da hanzarin yanzu suna ina?

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya samu nasarar lashe zaben 2015 da taimakon jama'ar Nigeria musamman talakawa da suka yarda da cewar zai kawo masu gagarumin canji, cikinsu kuwa harda mata masu dauke da juna biyu, wadanda suka bar dakin nakuda suka fito don zabarsa.

Da ya ke jawabi ga al'ummar Nigeria mazauna kasar Amurka, daga cikin ziyarar da ya kai New York don halartar babban taron kasa da kasa na majalisar dinkin duniya UNGA73, shugaban kasar ya ce idan har aka sake bashi dama a 2019, zai tabbatar ya kara kaimi akan wanda ya nuna yanzu.

Ya buga misali da cewa a lokacin da ya ke shugabantar gidauniyar PTF, sun gina titi daga Legas zuwa Abuja zuwa Onitsa har zuwa Fatakwal, sai dai ya ce tun daga wannan lokacin har zuwa 2015 gwmanatin PDP ba ta gina wani titi mai wannan tsawon ba.

Ganawar Buhari da al'ummar Nigeria mazauna kasar Amurka
Ganawar Buhari da al'ummar Nigeria mazauna kasar Amurka
Asali: Facebook

KARANTA WANNAN: Yan ta'adda sun kai sabon hari a sakatariyar jam'iyyar PDP a jihar Bayelsa

"Sun dade suna kira na da Baba Go Slow. Wadanda ke tafiya da hanzarin yanzu suna ina?"

"A 1983, jami'an soji suka taru suka bani mukamin shugaban kasa. Na garkame dukkanin 'yan siyasa a gidan kurkukuk, tare da sanar da su cewar su masu laifi ne har sai sun wanke kawunansu.

"Mun kwace kudade da kadarorin da suka sata, amma daga baya suka samu nasarar jefani a kurkuku, suka mayarwa barayin kasar abubuwan da suka sata, amma masu hassadar sun yi magana akan hakan?

"Sau 3 ina tsayawa takara; sau 3 ina zuwa kotu bayan anyi murdiyar sakamakon zaben akaina. Babu adalci a tare da su, amma na ce babu komai Allah na nan. A 2019, ba zan taba mantawa ba, kaso mafi tsoka daga wadanda suka tsaya min tsayin daka, talakawa ne suka tabbatar da ganin cewa an zabe ni kuma an bayyanani a matsayin wanda ya lashe zaben.

"Don haka ne ma har kullum nake alfahari kuma nake tutiya da cewar a 2019, hatta matan da ke halin nakuda za su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabeni kamar yadda wasunsu suka yi min a zaben 2015." a cewar Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel