2019: 'Dan Uwan Aisha Buhari ya kulla yarjejeniya da Nuhu Ribadu kan takarar Kujerar Gwamnan jihar Adamawa

2019: 'Dan Uwan Aisha Buhari ya kulla yarjejeniya da Nuhu Ribadu kan takarar Kujerar Gwamnan jihar Adamawa

Wani dan uwa ga uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, Mahmud Halilu, wanda ke neman takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar APC, ya bayyana cewa zai kulla wata yarjejeniya mai muhimmanci da Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, Halilu zai kulla yarjejeniya da tsohon shugaban hukumar ta EFCC domin hada karfi da karfi wajen cin nasara kan gwamnan jihar, Jibrilla Bindow, yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar da za a gudanar a gobe Asabar.

A yayin ganawarsa da manema labarai cikin birnin Yola a ranar da ta gabata, Halilu ya jaddada muhimmancin kulla yarjejeniya da alaka mai karfin gaske tsakanin sa da Ribadu domin sauya gwamnati a jihar.

2019: 'Dan Uwan Aisha Buhari ya kulla yarjejeniya da Nuhu Ribadu kan takarar Kujerar Gwamnan jihar Adamawa
2019: 'Dan Uwan Aisha Buhari ya kulla yarjejeniya da Nuhu Ribadu kan takarar Kujerar Gwamnan jihar Adamawa
Asali: Depositphotos

A halin yanzu manema takarar biyu na ci gaba da ganawa da juna domin kulla yarjejeniya ta daya ya janyewa daya da kuma marawa daya baya a yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar kamar yadda Halilu ya bayyana.

KARANTA KUMA: Kungiyar 'Kwadago ta hana Jirage tashi a Filin Jirgin sama na jihar Legas

Yake cewa, wannan yunkuri ya bayu ne a bisa bukatar sauya gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Bindow da ta jefa al'ummar jihar cikin kangi na wahalhalu har na tsawon shekaru uku.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wani manemi takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, Marcus Gundiri, ya janye takararsa a kwana-kwanan domin goyon bayan surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel