Wata kungiya za ta shiga Kotu da Shugaban INEC saboda an sayawa Shugaban kasa Buhari fam

Wata kungiya za ta shiga Kotu da Shugaban INEC saboda an sayawa Shugaban kasa Buhari fam

Wata Kungiya mai zaman kan-ta ta shirya maka Shugaban Hukumar zabe na kasa watau INEC a gaban Kotu a dalilin fam din takarar da aka sayawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kwanakin baya.

Wata kungiya za ta shiga Kotu da Shugaban INEC saboda an sayawa Shugaban kasa Buhari fam
Kungiyar Voters Rights International za ta shiga Kotu da Buhari
Asali: Depositphotos

Kungiyar ta Voters Rights International ta na karar Shugaban Hukumar zabe na kasa Mahmood Yakubu ne saboda an sayawa Buhari wanda shi ne ‘Dan takarar Jam’iyyar APC fam. Kungiya ta na ganin hakan ya sabawa dokar kasa.

Shugaban wannan Kungiya Mista Jezie Ekejiuba, wanda babban Lauya ne da ke kare hakkin Jama’a ya bayyana cewa zai ruga Kotu ya nemi a dakatar da Buhari daga takara domin Kungiyar da ta saya masa fam ba ta da rajista.

Jezie Ekejiuba yace Hukuma ba ta san da zaman NCAN wanda ta sayawa Muhammadu Buhari takardar tsayawa takarar Shugaban kasa a APC ba. Ekejiuba yace a dokar kasa ma, mutum ne kurum zai iya sayen fam din sa da kan sa.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta sake yin wala-wala da ranakun zaben ta

Sashe na 131 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 yace mutum zai saye fam din takara ne da kan sa a karkashin Jam’iyya mai rajista. Don haka ne wannan Kungiya ta ke ganin cewa har yanzu APC ba ta saidawa kowa fam ba.

Wata kungiya ce mai suna NCAN ta saye fam a madadin Shugaba Buhari domin ya zarce a 2019. Sai dai wannan Lauya yace hakan ya sabawa dokar kasa don haka ya nemi Kotu ta cire Buhari daga cikin masu neman takara gaba daya.

A baya dai kun ji cewa dokar kasa tace bai halatta ‘Yan takara su karbi gudumuwar da ta haura Naira Miliyan 1 daga mutum guda ba. Sai dai kwamitin yakin neman zaben Buhari tace ba ta karya doka ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel