Kwankwaso, Sule Lamido da Saraki sun yi kus kus game da zaben fidda gwani na PDP

Kwankwaso, Sule Lamido da Saraki sun yi kus kus game da zaben fidda gwani na PDP

A yayin da zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a karkashin inuwar lemar jam’iyyar PPD ke karatowa, yan takarkaru da sauran shuwagabannin jam’iyyar sun nuna bacin ransu game da garin da jam’iyyar ke kokarin shirya zaben a can.

Majiyar Legit.ng dangane da haka ne shugaban majalisar dattawa, kuma dan takarar shugaban kasa a PDP, Sanata Bukola Saraki ya kai ziyara ga tsohon gwamnan jahar Jigawa, wanda shima ke takarar shugabancin kasarnan a PDP, Sule Lamido a garin Dutsen jahar Jigawa.

KU KARANTA: Ma’aikata a jahar Kaduna sun yi fatali da batun shiga yajin aikin kungiyar kwadago

Haka zalika shima madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai kwatankwacin wanna ziyarar ga Sule Lamido a garin Dusten jahar Jigawa domin tattauna yadda zasu hana kai zaben fitar da yan takarar PDP daga garin Fatakwal zuwa wani gari na daban.

A yayin ziyarar tasa, Saraki ya gana da wakilan jam’iyyar PDP na jahar Jigawa a sakatariyar jam’iyar dake Duste, wanda sune zasu yi zaben fitar da yan takara, inda yayi musu jawabi da harshen Hausa,ya bayyana musu burinsa na ganin ya zama shugaban kasar Najeriya a 2019.

Kamar yadda fuskokinsu ya nuna, yayan jam’iyyar ta PDP sun yi mamakin yadda Saraki yayi musu jawabi da harshen Hausa, kuma sun nuna farin cikinsu game da haka kamar yadda daraktan yakin neman zaben Saraki, Mohammed Wakil ya bayyana.

A jawabinsa, Wakil ya bayyana godiyarsa da ta maigidansa da ma na kafatanin jagororin yakin neman zaben Sanata Abubakar Bukola Saraki game da yadda suka basu kyakkyawar tarba a, sa’annan ya kara da cewa bay akin neman zabe suka zo ba, sun zo ne domin gaishe da wakilan.

Shima a yayin ziyarar tasa, madugun Kwankwasiyya ya samu ganawa da daliget na jam’iyyar PDP, sa’annan ya gana da Sule Lamido, sai dai ya bayyana ma manema labaru cewa bai samu damar yin tsawon tattaunawa da Sulen ba.

Majiyarmu ta ruwaito jim kadan bayan tafiyar Saraki da Kwankwaso, sai ga wani dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP na daban, tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa shima ya isa garin Dutse inda ya gana da daliget, amma bai isa gidan Sule Lamido ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel