Matasa fiye da 35000 sun shiga Katsina domin goyon bayan su ga Buhari a 2019

Matasa fiye da 35000 sun shiga Katsina domin goyon bayan su ga Buhari a 2019

Mun ji cewa akalla matsa 35, 000 ne karkashin Kungiyar Buhari Campaign Organisation da ke taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari yakin neman zabe su ka sha alwashin mara masa baya a 2019.

Matasa fiye da 35000 sun shiga Katsina domin goyon bayan su ga Buhari a 2019
Wasu tarin Matasa su na neman Buhari ya zarce a karagar mulki
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Matasa 35, 560 daga Yankin Arewacin Katsina sun shiga Daura inda nan ne Mahaifar Shugaban kasa Buhari domin nuna goyon bayan su ga mulkin Buhari su na mai neman ya zarce.

Shugaban wannan Kungiyar ta Matasa Mohammed Mashi yayi jawabi a Mahaifar Shugaba Buhari inda ya bayyana dalilin da ya sa su ke neman a sake zaben Shugaban kasar. Mashi yace Buhari yayi abin a-zo-a-gani a shekara 3.

Mohammed Mashi yace an ga aiki a kasa wajen gina titi da kuma aikin layin dogo da kuma yaki da barna da bangaren tsaro. Mashi yace su na sa rai idan aka kuma zaben Shugaba Buhari a 2019, abubuwa su kara mikewa a Kasar nan.

KU KARANTA: Gwamna Masari ya yi wa Buhari alkawarin kuri'u Miliyan 2.5 daga Katsina

Kungiyar tayi alkawarin cewa Shugaban kasar zai samu kuri’a miliyan guda a Yankin na Arewacin Katsina inda ya fito. Yankin dai yana da Kananan Hukumomi 12 kuma Jam’iyyar APC ce da karfi kamar yadda zaben kwanaki ya nuna.

Yankin dai na Katsina ta Arewa na kunshe da Garuruwan Daura, Maiadua, Sandamu, Zango, Baure, Mashi, Mani, Ingawa, Bindawa, Kankiya, Kusada da kuma Dutsi. Akwai Kananan Hukumomi 34 ne gaba daya a Jihar.

Malam Abdulfatah Daura wanda shi ne Jagoran wannan Kungiyar a Garin Daura yace Shugaban kasar zai samu tarin kuri’u a gida. A farkon 2019 ne dai za ayi zaben Shugaban kasa a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel