2019: APC ta haramtawa Mama Taraba takarar gwamna

2019: APC ta haramtawa Mama Taraba takarar gwamna

Jam'iyyar APC mai mulki ta haramtawa wasu 'ya'yanta shiga takarar gwamna ciki har da ministan harkokin mata, Aisha Alhassan da ministan sadarwa, Adebayo Shittu.

Kwamitin gudanarwan na jam'iyyar ne ta dauki wannan matakin sakamakon rahoton da da samu daga kwamitin tantance 'yan takarar gwamna na jam'iyyar.

Mrs Aisha, wadda aka fi sani da Mama Taraba tana son takarar kujerar gwamna na jihar Taraba ne yayin da Mr Shittu Adebayo shi kuma yana niyyar takarar gwamna ne a jihar Osun.

2019: APC ta haramtawa Mama Taraba takarar gwamna
2019: APC ta haramtawa Mama Taraba takarar gwamna
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yajin aiki: Ku fitar da ran samun albashi a kan lokaci - Babban akawun tarayya ga ma'aikata

Duk da cewa kwamitin ta soke takarar Mr Shittu ne saboda bashi da shaidar kammala NYSC ko kuma hidimar kasa, kwamitin ba ta bayar da dalilin ta na soke takarar Mrs Alhassan ba.

Wasu masu neman takarar gwamnan da kwamitin bata tantance sun hada da Osiobe Eric Okotie (Delta), Ejikeme Ugwu (Enugu), Ibrahim Mohammed Mera (Kebbi), Danladi Envulu-Anza Halilu (Nasarawa) da Abubakar Mamma Jiya Maaji (Niger).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel