Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihar

Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihar

Za ku ji cewa akwai jiga-jigan kasar nan da a halin yanzu su na can kudancin kasar nan domin zaman kirdado na sakamakon zaben gwamnan jihar Osun da aka sake gudanarwa a yau Alhamis kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata bai inganta ba a yayin da hukumar zabe ta kasa watau INEC tayi watsi da shi sakamakon dambarwar da ta auku yayin gudanar sa kama daga tashin-tashina ta 'yan baranda da kuma kwacen akwatin zabe.

Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihar Osun
Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihar Osun
Asali: UGC

Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihar Osun
Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihar Osun
Asali: Twitter

A yayin da ake ci gaba da zaman kirdadon sakamakon zaben gwamnan jihar da yau hukumar zabe ta sake gudanarwa, akwai wasu jiga-jigan kasar nan da suka kwashi kafafunsu har zuwa jihar domin kashe kwarkwatar idanunsu da hausawa kan ce gani ya kori ji da zasu kasance ganau ba jiyau ba.

Ire-iren wannan jiga-jigai da suka yi tattaki har zuwa jihar ta Osun sun hadar da; gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da takwaransa na jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, Ministan watsa labarai da al'adu; Lai Muhammad, zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da sauransu.

KARANTA KUMA: Abuja da wasu Jihohi 4 da ka iya fuskantar girgizar 'Kasa

Gwamnan jihar ta Osun, Rauf Aregbesola tare da Mataimakin sa, Sanata Iyiola Omisore, sun karrama wannan manyan baki yayin da suke zaman kirdadon sakamakon zaben a fadar gwamnatin su dake babban birnin jihar na Osogbo.

Legit.ng ta ruwaito cewa, akwai kyakkyawan zato dan takarar jam'iyyar APC, Alhaji Gboyega Oyetola, shi zai lashe wannan zabe da yake kan gaba wajen samun nasara yayin da hukumar INEC ke ci gaba da kidayar kuri'u da bayyana sakamakon ta dalla dalla.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel