Shugaba Buhari yace a kula da yaduwar muggan makaman Nukiliya

Shugaba Buhari yace a kula da yaduwar muggan makaman Nukiliya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwar shi akan rashin hanzarin wasu kasashe gurin kawar da ma'adanar makaman kare dangin su.

- Hakkin kowa ne tabbatarwa da samar da zaman lafiya, adalci da kuma cigaba ga mutane

- Kusan karni daya kenan da duniya ta fuskanci bala'in makamin kare dangi amma har yau akwai illolin shi

Shugaba Buhari yace a kula da yaduwar muggan makaman Nukiliya
Shugaba Buhari yace a kula da yaduwar muggan makaman Nukiliya
Asali: UGC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwarshi akan yanda wasu kasashe suka kasa hanzari kawar da ma'adanar makaman kare dangin su.

Yayi maganar ne a birnin New York, a taron tunawa tare da karfafa kawar da makaman kare dangi na duniya.

Ya tunatar da duniya cewa hakkin samar da zaman lafiya, adalci da kuma yaduwar tattalin arziki ya rataya ne a wuyan kowa. Ya nuna bukatar batar da makaman kare dangi kamar yanda akayi yarjejeniya.

DUBA WANNAN: Yajin aiki a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda mai bada shawara ta fannin tsaro, Babagana Monguno, ya wakilta yace Idan zamu lura, kusan karni daya kenan da duniya ta fuskanci bala'in makamin kare dangi na farko amma har yau muna fuskantar illolin shi. Ba wai wadanda abin ya shafa ba, duk duniya ce ake fama da illar.

Ya kara da cewa, cigaba da ajiye makaman kare dangi barazana ce ga dukkan mutane. Kudin cigaba da adana, tare da sabunta su don dacewa da zamani kadai ya isa a karfafa habakar arziki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel