Yajin aiki: Zamu hana jiragen sama sauka da tashi daga Najeriya – Kungiyar kwadago

Yajin aiki: Zamu hana jiragen sama sauka da tashi daga Najeriya – Kungiyar kwadago

Hadaddiyar kungiyar kwadago daya kunshi NLC da TUC sun bayyana cewa zasu rufe duk wasu filayen sauka da tashin jirage dake Najeriya don tabbatar da duk ma’aikata sun bi umarnin kungiyar na shiga yajin aikin dindindin a Najeriya.

Mjaiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar kwadago na jahar Legas, Amechi Asugwuni ne ya tabbatar da wannan umarni na uwar kungiyar kwadago ta kasa a wata tattaunawa da yayi da yan jaridu a ranar Alhamis 27 ga watan Satumba a garin Legas.

KU KARANTA: Yajin aiki: Kungiyar likitocin Najeriya ta yi hannun riga da kungiyar kwadago

Asuguwni yace sun yi iya kokarinsu a zaman da wakilan kungiyar kwadago ta yi da gwamnatin tarayya a ranar Laraba don ganin ba’a shiga yajin aikin ba, amma gwmanati taki yarda ta biya musu bukatunsu, don haka aka tashi barambaram.

“Mun shiga wannan yajin aiki ne don ganin cewa ma’aikacin Najeriya ya samu ingantaccen karin albashi, kuma muna fatan wannan gwagwarmayan da muke zai kawo samar da sakamakon da muke muradin gani, don haka muka zauna da gwamnati a jiya, amma an tashi barambaram saboda sun kasa biya mana bukata.

“Amma na samu labarin fadar shugaban kasa ta gayyaci shuwagabannin kungiyar kwadago don sake tattauna matsalar, bamu da matsala da zaman sulhu ko na tattaunawa, amma muna da matsala da rashin samun biyan bukata.

“Don haka zamu zagaya jahar Legas don tabbatar da mun kulle duk wata cibiya, haka zalika idan filayen sauka da tashin jirage a Najeriya sun yi aiki yau, toh daga gobe ba zasu yi aiki ba, babu jirgin da zai kara sauka ko tashi daga Najeriya, saboda zamu kulle duk wani fili dake Najeriya.” Inji shi.

Kungiyar kwadago ta kaddamar da yajin aikin ne saboda bukatar data mika ma gwamnatin don ta biya ma’aikatan Najeriya dubu hamsin da shida a matsayin karancin albashi, sai dai ta zargi gwamnati da jan kafa akan maganan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel