Buhari ya baiwa majalisar dinkin duniya shawarar yadda za’a magance fadan Isra’ila da Falasdin

Buhari ya baiwa majalisar dinkin duniya shawarar yadda za’a magance fadan Isra’ila da Falasdin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bacin ransa game da tabarbarewar zaman lafiya da aka cigaba a yankin gabas ta tsakiya sakamakon rikici tsakanin Falasdinawa da Isara’ilawa tun bayan zaman majalisa na shekarar data gabata.

Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne a yayin dayake gabatar da jawabinsa a taron koli na majalisar dinkin duniya karo na 73 daya gudana a birnin New York na kasar Amurka, shelkawatar majalisar din dinkin duniya, UN.

KU KARANTA: Yajin aiki: Kungiyar likitocin Najeriya ta yi hannun riga da kungiyar kwadago

Haka zalika shugaba Buhari ya sanar da shuwagabannin kasashen Duniya sama da dari da suka halarci taron hanyoyin daya kamata a wabi wajen kawo karshen rikicin da aka kwashe shekara da shekaru ana fafatawa, inda yace a baiwa kowa kasarsa, shine ginshikin zaman lafiya a yankin.

“Matsalar gabas ta tsakiya na cigaba da ruruwa tare da kazanta tun bayan zaman da mukayi a bara, Najeriya na cigaba da kira ga Falasdinawa da Isra’ilawa dasu kawar da son zuciya domin samar da kyakkyawar yanayin zaman lafiya, adalci da tabbatar da tsaro a yankin

“Matsalar yan gudun hijira na cigaba da ta’azzara a yankin Gaza sakamakon amfani da makamai da bangarorin keyi, don haka muke kira ga kasashen dasu koma ga matakan da majalisar dinkin duniya ta dauka don kawo karshe rikicin.

“Matsayin Najeriya anan shine a samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu, na Falasdin dana Israila, ta hanyar tattaunawa ba tare da barazana ko nuna fin karfi ba, muna sane da cewa wannan rikici na da dadden tarihi, kuma an dade ba'a samo bakin zaren ba, amma hakan ba zai sa mu karaya ba.” Inji shi.

Daga karshe Buhari yace ayi duba ga yadda kasashen Ethopia da Eritrea suka kawo karshen yake yaken dake tsakaninsu, wanda aka kwashe shekaru da dama ana fafatawa, don haka yace yana ganin idan kowa nada niyyar samar da zama lafiya, za’a samar da shi a yankin gabas ta tsakiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel