Yabon gwani: Sarauniyar Ingila ta ba Dakta Abdullahi Balarabe Shehu lambar yabo

Yabon gwani: Sarauniyar Ingila ta ba Dakta Abdullahi Balarabe Shehu lambar yabo

A makon jiya ne mu ka samu labari daga Daily Trust cewa wani Likita da ake ji da shi a Kasar Ingila watau Dr. Abdullahi Shehu ya samu karramawa da yabon girma daga wajen Sarauniyar Ingila.

Abdullahi Shehu asalin sa mutumin Yakassai ne a Jihar Kano wanda ya tafi Ingila shekaru fiye da 30 da su ka wuce. Dr. Shehu ya fara aiki ne a wani asibiti da ke Coventry tun a 1993 inda har ya zama babban Likitan kwakwalwa ya kuma rike mukamai da-dama.

Dr. Abdullah Shehu yayi karatun sa ne da farko a Jami’ar Ahmad Bello ta Zariya kafin ya bar Kasar. Yanzu Dakta Shehu yana cikin Likitocin kwakwalwa da ake ji da su a kaf Kasar Birtaniyya da ma Duniya gaba daya don haka Sauraniya ta ba sa lambar girma ta MBE.

KU KARANTA: Wani hazikin Matashi 'Dan Najeriya ya ciri tuta a fadin Duniya

Dr. Shehu Mutum ne Masanin gaske kuma a harkar addini domin shi ne Shugaban Likitoci Musulmai da ke Kasar Ingila. Sarauniyar ta ba Dakta Shehu wannan lamba ne saboda kokarin da ya yi wa Coventary da kuma Kasar Birtaniya gaba daya.

Ahmed Yakasai wanda shi ne Shugaban Kungiyar PSN ta Najeriya ya taya ‘Dan uwan aikin na sa kuma tsohon Abokin sa murnar wannan mataki da ya kai a rayuwa. Dr. Shehu Yaya ne wajen tsohon Shugaban Injinioyin Najeriya watau Musatafa B. Shehu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel