Ruwa baya tsami banza: Cacar baki ya kaure tsakanin wani gwamna da mataimakinsa

Ruwa baya tsami banza: Cacar baki ya kaure tsakanin wani gwamna da mataimakinsa

Rikici tsakanin gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha da mataimakinsa, Eze Madumere ya girmama tun bayan hukuncin wata babbar kotun tarayya data soke tsige Mista Eze daga mukaminsa da gwamna Rochas ya yi, inji rahoton Daily trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a kwanakin baya ne gwamnan jahar tare hadin bakin Alkalin Alkalan jahar da majalisar dokokin jahar suka taru suka yi kutunkutun data kai ga an tsige mataimakin gwmana Madumere akan wai baya zuwa aiki da wuri da sauran zarge zarge.

KU KARANTA: Toh fa! Malaman da El-Rufai ya sallama daga aiki sun gabatar masa da Al-kunuti

Sai dai tun bayan wannan hukunci na babbar kotun tarayya, sai rikicin nasu ya dauki sabon salo, inda Mista Eze madumere ke ikirarin har yanzu shine mataimakin gwamnan jahar Imo, shi kuma Gwamna Rochas na ikirarin cewa abin gama ya gama.

Ruwa baya tsami banza: Cacar baki ya kaure tsakanin wani gwamna da mataimakinsa
Rochas da Eze
Asali: UGC

A ranar Laraba, 27 ga watan Satumba ne Eze ya fitar da wata sanarwa yana tabbatar da mukaminsa, inda yace hukuncin kotun ya tabbatar da gaskiyarsa, jim kadan sai gwamnan jahar ta bakin mai magana da yawunsa, Sam Onwuemeodo ya karyata Eze inda yace sun daukaka kara don haka yana nan a matsayin korarre.

“Bamu tanka hukuncin da ake cewa babbar kotun Najeriya ta yanke ba, saboda muna jiran samun cikakken rahoton hukuncin ne daga kotun don yin nazari akansa, amma a yanzu mun samu wannan rahoto, kuma mun nazarceshi, amma bamu gamsu da hukuncin ba. Don haka mun daukaka kara.” Inji shi.

Sai dai Gwamna Rochas ya bayyana Eze a matsayin rudadde wanda a rasa madafa, inda yace “Ta yaya mutum zai ce shine mataimakin gwamna, kuma dan takarar gwamnan jahar a inuwar jam’iyyar APC bayan bai wuce awanni 48 ba kafin a gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar ba.

Daga karshe gwamnan ya nuna bacin ransa game alakar dake tsakanin yan takarar gwamnan jahar da suka hada da tsohon gwmanan jahar, Ikedi Ohakim na jam’iyyar APGA, da Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP, inda yace da gangan yayi haka don ya ci mutuncin gwamnan daya taimakeshi a rayuwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel