Toh fa! Malaman da El-Rufai ya sallama daga aiki sun gabatar masa da Al-kunuti (Hotuna)

Toh fa! Malaman da El-Rufai ya sallama daga aiki sun gabatar masa da Al-kunuti (Hotuna)

Anyi wani gangamin wasu mutane masu ra’ayi dake ganin gwamnatin jahar Kaduna a karkashin shugabancin Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya zaluncesu ta hanyar rabasu da aikin da suke yin a koyawar, a garin Zaria ta jahar Kaduna.

Legit.ng ta ruwaito wannan gangami kunshi tsofaffin Malaman dake koyarwa a makarantun Firamarin jahar Kaduna da Gwamna El-Rufai ya sallamesu daga aiki bayan sun fadi jarabawar daliban aji hudu da gwamnatin ta shirya musu a cewar gwamnan.

KU KARANTA: Yajin aikin dindindin: An goga gemu da gemu tsakanin Ministan kwadago da kungiyoyin kwadago

Toh fa! Malaman da El-Rufai ya sallama daga aiki sun gabatar masa da Al-kunuti (Hotuna)
Malaman
Asali: Facebook

Wannan ne dalilin daya sanya tsofaffin malaman hada kawunansu, tare da gudanar da sallar alkunuti a babban filin sallar idi na Zaria, dake gab da kofar doka, inda suka munanan addu’o’i game da gwamnatin jahar Kaduna da jagorarta.

A yayin wannan sallar alkunuti, an hangi wasu daga cikin Malaman dauke da takardun nuna ba’a tare da gwamnatin jahar Kaduna, daga cikinsu akwai mau cewa “El-Rufai bakin bayahude ne” “Bamu babu azzalumin shugaba”, “Jam’iyyar APC ta Kuduna mai kashe mutane ce” “Shugaba muke so ba mai takalmin karfe ba”, “Bama son zaben daliget saboda gwamnan bada gaske yake ba.”

Toh fa! Malaman da El-Rufai ya sallama daga aiki sun gabatar masa da Al-kunuti (Hotuna)
Malaman
Asali: Facebook

A wani labadin kuma, gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da cika adadin sabbin malaman firamari data dauka aiki zuwa dubu ashirin da biyar cif cif bayan daukan Malamai guda dubu goma sha 12 a baya, yanzu kuma ta sake daukan malamai guda goma sha uku don maye gurbin malamai dubu ashirin da biyu data sallama.

Gwamnatin ta bayyana cewa yawancin sabbin malaman data dauka masu digiri ne, kuma akwai masu digirina biyu, sai sauran dake dauke da kwalin NCE.

Toh fa! Malaman da El-Rufai ya sallama daga aiki sun gabatar masa da Al-kunuti (Hotuna)
Malaman
Asali: Facebook

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel