B’araka a Kwankwasiyya: Aminu Dabo ya bijire ma Kwankwaso ya yanke tikitin takara

B’araka a Kwankwasiyya: Aminu Dabo ya bijire ma Kwankwaso ya yanke tikitin takara

B’araka a Kwankwasiyya: Aminu Dabo ya bijire ma Kwankwaso ya yanke tikitin takara
B’araka a Kwankwasiyya
Asali: UGC

Guda daga cikin jigogin taffiyar Kwankwasiyya dake karkashin shugabancin tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Aminu Dabo ya bijire ma shugabannasu yayi gaban kansa, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba, 26 ga watan Satumba ne Aminu Dabo ya kalubalanci Kwankaso game da takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, inda shima ya garzaya ofishin uwar jam’iyyar dake Abuja ya yanki tikitin tayawa takarar gwamnan jahar Kano.

KU KARANTA: Yajin aikin dindindin: An goga gemu da gemu tsakanin Ministan kwadago da kungiyoyin kwadago

Haka zalika shima tsohon mataimakin gwamnan jahar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya yanke wannan tikiti na tsayawa takarar gwamna a babban ofishin jam’iyyar PDP dake Abuja, duk da umarnin da jagoran Kwankwasiyya ya bayar.

Wadannan yan siyasan kuma jigogi a tafiyar Kwankwasiyya sun yanki tikitin ne don kalubalantar kama karya da suke ganin Sanata Kwankwaso yayi musu game da fitar da sunan surukinsa, Abba K Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan jahar Kano a inuwar jam’iyyar PDP.

Majiyarmu ta tattauna da wani makusancin Dabo dake cewa: “Ba daidai bane kace babu wanda zai iya zama gwamna face Abba, don haka Aminu ya yanki wannan tikiti don nuna ma duniya cewa shima ya cancanci shugabancin Kano, tsayar da Abba son kai ne, kuma zamu yake shi.”

A wani labarin kuma, daga karshe Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga birnin Kano, inda ya gana da masoya da abokan arziki, sai dai bai wani dade bay a kama hanyarsa ta komawa jahar Kaduna, inda ya samu mafaka tun bayan barkewar rikicinsa da Gwamna Ganduje.

Sai dai a yayin da ya kai wannan ziyara jahar Kano, gwamnan jahar, Abdullahi Umar Ganduje yana can jahar Osun a matsayinsa na shugaban yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jahar dake gudana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel