2019: Wata kungiya ta mamaye gaban ofishin majalisar dinkin duniya saboda Buhari, hoto

2019: Wata kungiya ta mamaye gaban ofishin majalisar dinkin duniya saboda Buhari, hoto

Wata sabuwar kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasar Amurka (Nigerian-America Development Advocate) sun mamaye gaban ofishin majalisar dinkin duniya (MDD) domin nunawa duniya goyon bayansu ga takarar shugaba Buhari a zaben 2019.

Mutanen sun isa kofar shiga ofishin majalisar dinkin duniyar sanye da rigunan yakin neman zaben Buhari a shekarar 2019, sannan suna dauke da hotonsa.

Kungiyar ta ce ta zabi mamaye gaban ofishin majalisar dinkin duniyar ne saboda su sanar da duniya cewar Najeriya bat a taba yin dacen shugaba kamar Buhari ba.

Shugaba Buhari da ragowar shugabannin kasashen duniya na kasar Amurka domin halartar taron majalisar dinkin duniya.

2019: Wata kungiya ta mamaye gaban ofishin majalisar dinkin duniya saboda Buhari, hoto
Wata kungiya ta mamaye gaban ofishin majalisar dinkin duniya saboda Buhari
Asali: Twitter

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar Teneo Intelligence, wata cibiyar bincike mai zaman kanta a garin New York na kasar Amurka ta bayyana cewar zaben gwamnan jihar Osun na ranar Asabar ya nuna cewar shugaba Buhari zai iya faduwa zaben shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Yajin aiki: An kasa cimma matsaya tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago

A sakamakon binciken cibiyar da jaridar Bloomberg ta wallafa, Teneo ta bayyana cewar amma idan jam'iyyar APC ta hada kan 'ya'yanta tare da dinke barakar dake cikinta, to zasu kai ga nasara.

"Sakamakon zaben Osun ba kankanuwar illa gare shi ga tasirin takarar Buhari a 2019 ba. Akwai sako cikin abinda ya faru a zaben gwamnan jihar Osun. Jam'iyyar PDP ta hada kan 'ya'yanta, kuma 'yar manuniya ta nuna cewar idan za a yi zabe na gaskiya kamar na jihar Osun, APC zata yi shan kaye a zaben shekarar 2019," a cewar Malte Liewerscheidt na cibiyar bincike ta Teneo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng