Dr. Nasiru Gawuna yayi jawabi kan harkar noma a Jami’ar Bayero ta Kano

Dr. Nasiru Gawuna yayi jawabi kan harkar noma a Jami’ar Bayero ta Kano

Labari ya zo gare mu daga Daily Trust cewa sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano wanda aka nada kwanaki yayi magana game da matsalar da aka samu a bangaren harkar noma a Najeriya.

Dr. Nasiru Gawuna yayi jawabi kan harkar noma a Jami’ar Bayero ta Kano
Nasiru Gawuna masani ne kuma Kwamishina a harkar noma
Asali: Facebook

Dr. Nasiru Yusuf Gawuna yayi magana game da yadda harkar gona ya tabarbare musamman a Arewacin Najeriya bayan irin tunbatsar da yankin yayi a baya a Duniya. Gawuna yace dogara kaco-kam da danyen man fetur ya jawo hakan.

Sabon Mataimakin Gwamnan na Kano yayi wannan jawabi ne a waken wani taro da aka shirya da ya shafi harkar noma a Jami’ar Bayero. Cibiyar noma na CDA ta Jami’ar Tarayyar da ke Kano ne ta shirya wannan zama domin ceto Kasar Afrika.

A zamanin baya, an san Jihar Kano da dalar gyada da kuma noman wake, a wancan lokaci dai da kayan amfanin gona Najeriya ta rika samun makudan kudin shiga kafin a gano danyen man fetur wanda ya shagwaba Kasar inji Nasiru Gawuna.

KU KARANTA: An dakatar da Magoya bayan Bindow daga shiga zaben fitar da gwani

Dr. Gawuna ya koka da yadda ake fama da yunwa da rashin cigaba duk da cewa Najeriya tana da mai. Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa manoman karkara na fama da matsaloli iri-iri a Najeriya musamman na rashin cigaba a noma.

Nasiru Gawuna yayi amfani da wannan dama wajen nuna cewa Gwamnatin nan na kokari wajen ganin an koma gona da gaske. Shugaban Jami’ar ta Bayero Farfesa Muhammad Yahuza Bello yayi jawabi a taron domin ganin an kawo cigaba.

A makon nan ne dai tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ya shiga Jihar Kano a gurguje domin ya gana da manyan PDP na Jihar domin ganin ya samu nasara takarar da yake yi na Shugaban kasa a Jam'iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel