Kiwon Lafiya: Kayan kamshi na girki na gyara lafiyar zuciya inji masana

Kiwon Lafiya: Kayan kamshi na girki na gyara lafiyar zuciya inji masana

- Ciwon zuciya na daya daga cikin cutuka masu kashe mutane

- Rage yawan kwalestarol a cikin jini na rage yuwuwar samun ciwo

- Kwalestarol kadan yana taka rawar gani gurin narkewar abinci

Kiwon Lafiya: Kayan kamshi na girki na gyara lafiyar zuciya inji masana
Kiwon Lafiya: Kayan kamshi na girki na gyara lafiyar zuciya inji masana
Asali: UGC

Ciwon zuciya na daya daga cikin cutuka masu kashe mutane har lahira a duk fadin duniya. Kowa zai so rage damar kamuwa da cutar. Amma daya daga cikin hanyoyin shine rage kwalestarol a jinin dan'adam.

Bincike ya nuna cewa a duk cikin maza biyu, daya na iya samun matsalar ciwon zuciya a rayuwar shi, haka zalika a duk mata uku, akwai yuwuwar daya daga ciki ta iya samun ciwon a rayuwar ta.

Duk da magani da kuma bayani akan kokarin kiyaye yawan kwalestarol a cikin jini, Idan ya taru yakan toshe jijiyoyin jini, wanda hakan kan toshe hanyoyin jini. Idan jijiyoyin zuciya kuwa basu samu isasshen jini ba, matsala takan faru.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya zarce kawai, samarin kasar nan

Kwalestarol sinadari mai amfani a jiki, yana kuma taka rawa gurin narkewar abinci. Amma Idan yayi yawa a jiki saboda dalilai kamar su qiba, gado, shan giya, rashin abincin da ya dace da sauransu, yakan kawo ciwon zuciya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel