Yajin aiki ya tabbata, an kasa cimma daidaito tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago
An kasa cimma dadidaito tsakanin kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da gwamnatin tarayya a kan fara yajin aiki gobe, Alhamis.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta kafe a kan shiga yajin aiki kamar yadda tayi niyya bayan gaza cimma wata sahihiyar matsaya a ganawar da tayi, ta tsawon sa’o’i, da gwamnatin tarayya.
An yi ganawar ne tsakanin kungiyar kwadago da ministan kwadago, Chris Ngige, da kuma kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin sake fasalin albashin ma’aikata a Najeriya.
A ranar Laraba ne Ngige ya tabbatarwa da kungiyar ta kwadago cewar gwamnatin tarayya zata dauki mataki a kan batun karin alabshin.
Sai dai shugaban kungiyar kwadago na kasa, Ayuba Wabba, y ace kungiyar ba zata janye kudirinta na shiga yajin aikin ba duk da tabbacin da ministan ya bayar.
Tuni dama kungiyar ta kwadago ta fitar da sanarwar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani da za a fara daga karfe 12:00 na daren yau, Laraba.
A cewar kungiyar ta NLC, shiga yajin aikin ya zama dole ne saboda gwamnatin tarayya ta ki daukan mataki a kan batun karin albashin ma’aikata duk da ta kafa kwamitin da zai yi hakan.
DUBA WANNA: 2019: Buhari zai iya faduwa zabe, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka
NLC na zargin gwamnatin tarayya da jan kafa dag an-gan a kan batun karawa ma’aikatan Najeriya albashi duk tsadar kayan masarufi da kullum ke karuwa.
Tun a kwanakin baya ne kungiyar NLC ta bawa gwamnatin tarayya wa'adin wa'adin kwanaki 14 (mako biyu) a kan ta bayyana matsayinta a kan batun karin albashin ma'aikata ko kuma su jagoranci ma'aikatan su fara yajin aikin jan kunne.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng