Rabuwar kai: Kwankwasiyya ta rabu gida biyu; Kwankwasiyya Amana da Kwankwasiyya Surukiyya

Rabuwar kai: Kwankwasiyya ta rabu gida biyu; Kwankwasiyya Amana da Kwankwasiyya Surukiyya

Da alamun rikici ya barke cikin gidan Kwankwasiyya yayinda wasu sun balle daga cikin kungiyar bisa ga zabin da shugabansu Kwankwaso yayi na surukansa.

Jaridar Daily Nigerian ta bayyana cewa wata majiya na kusa da Farfesa Abubakar ya bayyana cewa tsohon mataimakin gwamnan ya siya takardan takaran gwamnan ne domin fito-na-fito da Kwankwaso kan maganarsa cewa shi (Hafiz) da Salihu Takai basu cancanta ba.

Yace: “Kwankwasiyya ta rabe gida biyu, akwai kwankwasiyya Amana da Kwankwasiyya Surukiyya. Wadanda sukayi imanin cewa kungiyar Kwankwasiyya ba kungiyar yan surukai bane sun balle.”

“Ina tabbatar muku da cewa Kwankwasiyya Surikiyya za ta fashe saboda irin mutane maras amfani dake ciki.”

Rabuwar kai: Kwankwasiyya ta rabu gida biyu; Kwankwasiyya Amana da Kwankwasiyya Surukiyya
Rabuwar kai: Kwankwasiyya ta rabu gida biyu; Kwankwasiyya Amana da Kwankwasiyya Surukiyya
Asali: UGC

Wannan rabuwar kai ya fara ne lokacin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zabi surukinsa Yusuf Abba matsayin wanda zai yi takaran gwamnan jihar.

Daga ciki deleget 6,000 da zasuyi zabe a zaben fitar da gwanin jam’iyyar, Kwankwaso na da mabiya 1500.

Wani babban jigo a jam’iyyar, Ado Rano, ya bayyana cewa: “Akwai kura a gaban Abba Yusuf kafin ya iya zama dan takaran gwamnan karkashin jam’iyyar PDP. Saboda wajibi ne deleget su bi ta hannun kwamitin Mas’ud Doguwa.”

KU KARANTA: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi takaran gwamna

A ranan Litinin, yan sanda sun tarwatsa mambobin jam’iyyar PDP mabiya Kwankwaso yayinda suke taro a titin Sokoto Road.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Magaji Majia, ya ce hukuma ta dau matakin ne bisa ga umurnin kotu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel